Kalaman Shugaba Mubarak sun fusata 'yan adawa

Asalin hoton, Getty
An wallafa
Masu zanga- zanga a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira na kasar Masar, sun fusata dangane da jawabin shugaba Hosni Mubarak na kin sauka daga mulki har sai bayan an yi zabe a watan Satumbar bana.
Masu zanga- zangar sun yi ta kururuwa su na cewa "Tir da Mubarak" tare da daddaga takalmansu domin nuna fushinsu.
Da farko dai ana cikin farin ciki ne bayan da mutane da yawa suka yi tsammanin cewa shugaba Mubarak na shirin sauka daga kan karagar mulki.
Daya daga cikin 'yan adawa a kasar, Mohammed El- Baradei ya yi kira ga sojoji da su ceci kasar daga halin da ta shiga, inda ya yi gargadin cewa Masar na gab da fadawa cikin rikici.






















