Dole yarjejeniya da Iran ta kasance ta dindindin - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya ce abin da yake so kawai shi ne a cimma yarjejeniya ta dindindin da Iran.
A wata hira ta wayar tarho da tashar Fox News, shugaban Amurka ya ce: "Ban taɓa nuna sha'awa sosai kan sauya gwamnati ba. Wasu mutane suna magana kan sauya gwamnati, amma dole ne su bayyana abin da suke nufi da hakan, domin ni a zahiri na riga na kawar da gwamnatoci biyu.
"Rukuni na ɗaya da rukuni na biyu. Yanzu kuma muna mu'amala da Rukuni na Uku. Saboda haka za ku iya cewa wannan ita ce babbar ma'anar sauya gwamnati."
Trump ya ce halayen wannan rukuni na uku "ba su da bambanci sosai. Wataƙila sun fi hankali, amma kuma suna da matuƙar wahalar mu'amala. Muna kulla yarjejeniya da su, amma washegari sai su karya yarjejeniyar."
Ya ƙara da cewa yana son a cimma yarjejeniya da Iran wadda za ta daɗe tana aiki, "ta yadda ko da bayan shekaru huɗu, ko 15, ko 20, idan aka samu shugaban ƙasa marar ƙwarewa, Iran ba za ta iya mallakar makaman nukiliya ba."
Buɗe mashigar Hormuz ba abu ne mai wuya ba - Araghchi
Asalin hoton, Getty Images
Abbas Araghchi ya bayyana a wani bikin tunawa da Ranar Ƙasa ta Oman cewa: "Buɗe Mashigar Hormuz ba abu ne mai wuya ba, kuma abin da ake buƙata kawai shi ne Amurka ta amince da sharuɗɗan da Iran ta gabatar cikin adalci."
Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce hanya guda tilo ta fita daga halin da ake ciki a yanzu ita ce Amurka ta amince da "kurakuranta" tare da aiwatar da "alkawurran da ta ɗauka a baya." Ya kuma bayyana killace Iran ta ruwa da cewa "haramtacciya ce gaba ɗaya."
Araghchi ya kuma yi magana kan ziyarar wata tawaga daga Qatar zuwa Tehran a daren jiya, inda ya ce: "Irin wannan ziyara ba sabon abu ba ne ko kadan. Masu shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka na ci gaba da kai-komo, suna ganawa da bangarorin biyu tare da isar da shawarwari daga wannan bangare zuwa wancan."
A cewarsa, "Matsayinmu a fili yake karara, kuma muddin ba a cika bukatun Iran gaba ɗaya ba, batun sake buɗe Mashigin Hormuz ba shi da muhimmanci." Sai dai ya ƙara da cewa, "A ko da yaushe mun bayyana cewa a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa."
Sa'o'i kaɗan da suka gabata, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya tabbatar da cewa wata tawaga daga Qatar ta ziyarci Tehran a daren jiya, kuma ta koma Qatar bayan tattaunawar da ta ɗauki kusan awa biyu.
Yadda Musulunci zai haɓɓaka a Indiya cikin shekaru - Bincike
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Indiya za ta ci gaba da kasancewa ƙasar Hindu har tsawon shekaru da dama masu zuwa, amma ana hasashen cewa tsarin addininta zai canza a hankali.
Wani sabon bincike da Cibiyar Bincike ta Pew ta gudanar, wanda ya yi hasashen yawan mabiya addinin Hindu a duniya zuwa shekarar 2070, ya yi ƙiyasin cewa mabiya addinin Hindu za su kai kashi 76% na yawan al'ummar Indiya nan da lokacin, wanda ya ragu daga kashi 79% a shekarar 2020, yayin da kason Musulmi zai ƙaru daga kashi 15% zuwa kashi 20%.
An kama jagoran ƙungiyar fataucin miyagun ƙwayoyi a Mexico
Sojojin ƙasar Mexico sun tabbatar da cewa sun kama wani da ake zargi da kasancewa jagoran ƙungiyar fataucin miyagun ƙwayoyi, wanda ke cikin jerin mutane goma da hukumar binciken laifuka ta Amurka, wato FBI, ta fi nema ruwa a jallo.
An kama Fausto Isidro Meza Flores a jihar Sinaloa a daren Juma’a, lamarin da ya haddasa musayar wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da masu laifi, wanda ya sa masu kallon wani wasan ƙwallon baseball da ake yi a kusa suka rika tserewa domin neman mafaka.
Mutumin, wanda aka fi sani da lakabin Chapo Isidro, ana kyautata zaton shi ne shugaban ƙungiyar laifuka ta Meza-Flores, wadda ake kuma kira da Los Mazatlecos.
Ana zarginsa da aikata laifukan kisan kai, azabtarwa, da kuma karɓar kuɗin tilas daga mutane ta hanyar barazana.
Gwamnatin Amurka ta sanya tukuicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama shi.
Mun kai hari kan jirgin sama maras matuƙi na Amurka na 58 - IRGC
Sashen hulɗa da jama'a na Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ya sanar da cewa ya kai hari kan wani jirgin sama maras matuƙi na zamani kirar MQ-9 mallakin sojojin Amurka a sararin samaniyar mashigar Hormuz.
IRGC ta ce a cikin wata sanarwa cewa an gano jirgin, an tare shi, sannan tsarin kariyar sararin samaniya na rundunar ya kai masa hari kimanin awa guda da ta gabata.
Sanarwar ta yi ikirarin cewa wannan ne jirgin sama maras matuƙi kirar MQ-9 na Amurka na 58 da suka kai wa hari.
Ya zuwa yanzu, jami’an Amurka ba su fitar da wata sanarwa kan wannan ikirari ba, kuma babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da cewa an harbo jirgin saman.
An tsinci gawar tsohon ɗansanda da ke da alaƙa da binciken mafiya a Italiya
An tsinci gawar tsohon shugaban rundunar ƴansandan ƙasar Italiya da ake bincike a kansa kan zargin yunƙurin dakatar da sabon bincike game da kisan wani babban alƙalin yaƙi da mafia.
Gianni De Gennaro na daga cikin manyan jami’an tsaro masu tasiri a Italiya, kuma ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin da aka yi da ƙungiyar mafia ta Sicily, wato Cosa Nostra, a shekarun 1980 da 1990.
A baya-bayan nan masu gabatar da ƙara sun sanya shi ƙarƙashin bincike saboda zargin hana ko kawo cikas ga sabbin bincike da ake yi kan harin bam da aka yi da mota a birnin Palermo a shekarar 1992, wanda ya kashe alƙali Paolo Borsellino da wasu mutum biyar.
De Gennaro ya musanta aikata wani laifi.
Lauyansa ya shaida wa kafofin watsa labaran Italiya cewa ya kasance cikin matsananciyar damuwa saboda tilasta masa kare kansa daga zarge-zargen da yake ganin ba su da adalci.
Da na samu dama da na shawarci El-rufai ya tsaya a APC -Yahaya Bello
Asalin hoton, @OfficialGYBKogi
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa da har yanzu suna ci gaba da mu’amala da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya ba shi shawarar ya ci gaba da zama a jam’iyyar APC mai mulki.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, Yahaya Bello ya ce El-Rufai mutum ne mai basira da jajircewa wajen bin abin da ya yi imani da shi, amma da ya shawarce shi ya rage yin maganganun siyasa a bainar jama’a tare da ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar warware saɓanin da ke tsakaninsu ta hanyar siyasa.
Ya kuma ce El-Rufai na daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa APC, don haka ya kamata ya ci gaba da zama a jam’iyyar da ya taimaka wajen ginawa.
Ya ce kusan kimanin shekara huɗu da sadarwa ta katse a tsakaninsu, amma duk da haka ɗan takarar sanatan na Kogi ta Tsakiya ya ce har yanzu yana yi wa El-Rufai fatan alheri, yana mai cewa ba ya son ganin tsohon abokin aikinsa ya shiga matsalolin siyasa ko na shari’a.
Mun daƙile harin makamai masu linzami na Houthi a Riyadh - Saudiyya
Asalin hoton, Getty Images
Ƙawancen ƙasashen da Saudi Arabiya ke jagoranta a yaƙin da ake yi da mayaƙan Houthi a ƙasar Yemen ya ce ya harbo makamai masu linzami uku da aka harba zuwa birnin Riyadh.
Wannan shi ne karo na biyu cikin kwanaki kaɗan da mayaƙan Houthi suke kai hari kan babban birnin Saudi Arabiya.
Duk da sanarwar cewa an kakkaɓo waɗannan makaman tun kafin su kai ga hari, shaidu a Riyadh sun ce sun ji ƙarar fashe-fashe.
A kwanakin baya, hare-haren makaman roka da Houthi suka kai sun afkawa ginin hasumiya mafi tsayi a Riyadh, lamarin da ya lalata wasu benaye na ginin tare da jawo ɓarna ga gine-ginen da ke kusa da shi.
A ranar Juma’a, rundunar ƙawancen da Saudi Arabiya ke jagoranta ta kai hare-haren sama kan tashar jiragen ruwa ta Hodeidah da ke gabar Tekun Ja, tare da wasu wuraren da mayaƙan Houthi suke amfani da su.
Daga bisani, mayaƙan Houthi masu alaƙa da Iran sun ce za su ramawa waɗannan hare-hare, inda suka yi barazanar kai farmaki kan tashoshin jiragen ruwa na Saudi Arabiya da ke gabar Tekun Ja.
Har ila yau, sun gargadi kamfanonin jiragen sama da su guji amfani da sararin samaniyar Saudi Arabiya.
Kwastam ta dakatar da horon sabbin ma’aikata bayan tattaunawa da hukumar FCC
Asalin hoton, Facebook/Customsng
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da dakatar da shirin ɗaukan sabbin ma’aikata da ake gudanarwa a kwalejojin horaswar ta guda biyu, domin ba da damar ci gaba da tattaunawa da Hukumar Kula da Daidaito da Wakilcin Jihohi kan damuwa da aka nuna dangane da yadda aka ɗauki sabbin ma’aikatan.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwanturola Janar na Kwastam mai kula da Hulɗa da Jama’a, Abdullahi Maiwada, ya fitar, ya ce matakin ya biyo bayan ganawa da tattaunawar da aka yi tsakanin jami’an FCC da wata tawaga daga Hukumar Kwastam, inda ɓangarorin biyu suka jaddada ƙudurinsu na warware matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa mai ma’ana, fahimtar juna da kuma ci gaba da haɗin gwiwa.
Sanarwar ta ce Kwanturola Janar na Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya sake tabbatar da aniyar hukumar ta ci gaba da yin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati domin kare muradun ƙasa baki ɗaya.
"Muna da cikakken yaƙinin cewa tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati su ne hanya mafi dacewa wajen magance duk wata matsala tare da tabbatar da gaskiya da adalci," in ji Adeniyi.
Ya kuma yaba wa FCC bisa rawar da take takawa wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa, adalci da daidaiton wakilci a cikin nade-naden mukaman gwamnati da kuma tabbatar da bin ƙa’idar daidaiton jihohi kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.
"Za mu ci gaba da yin aiki cikin gaskiya da riƙon amana tare da neman hanyoyin da za su ƙara ƙarfafa amincewar jama'a da kuma tabbatar da ingantaccen gudanar da ayyukanmu," in ji sanarwar.
Ana zargin Boko Haram da jefa bama-bamai a hasumiyar lantarki a Najeriya
Asalin hoton, Boko Haram
Wasu da ake zargin mambobin Boko Haram ne sun tayar da bama-bamai a kan manyan hasumiyoyin wutar lantarki guda biyu a Jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya kwanaki huɗu da suka gabata. Kwamishinan ƴansandan jihar, Adamu Abdullahi Elleman, ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.
Haren ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana agogon ƙasar a ranar 17 ga Nuwamba, inda ya shafi hasumiyoyin da ke kan layin wutar lantarki da ke haɗa Madatsar Ruwa ta Kainji da Osogbo.
Wuraren da abin ya shafa suna kusa da ƙauyen Kanti a ƙaramar hukumar Mashegu da kuma ƙauyen Kanya a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja.
Jami’an tsaro sun tura kusan jami’ai 100 masu yaƙi da ta’addanci zuwa yankunan domin kare al’ummomin da ke kusa da wuraren da abin ya shafa tare da dakile yiwuwar ƙarin hare-hare.
An kuma sanar da kamfanin wutar lantarki game da lamarin, kuma an fara aikin gyaran kayayyakin da suka lalace.
Wani rahoton tsaro na farko ya nuna cewa fashewar ta haifar da fargaba tsakanin mazauna yankin, kuma ana zargin maharan sun kai harin ne da nufin kawo cikas ga isar da wutar lantarki daga Madatsar Ruwa ta Kainji.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar wasu sassan Jihar Neja, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke kai hare-hare kan al’ummomi, sace mutane tare da yin barazana ga muhimman ababen more rayuwa.
An ƙona gidajen magoya bayan tsohuwar Firaministan Bangladesh Sheikh Hasina
Mahukuntan Bangladesh sun tura ɗaruruwan ƙarin jami’an rundunar tsaro ta farin kaya a ranar Asabar, bayan da aka kai hare-hare da ƙone-ƙone tare da lalata gidaje da dama na magoya bayan tsohuwar Firaminista, Sheikh Hasina.
Sheikh Hasina ta sha alwashin komawa ƙasar daga Indiya a wata mai zuwa, duk da cewa an yanke mata hukuncin kisa ba tare da halartarta ba kan kisan masu zanga-zangar shekarar 2024.
Aƙalla mutum huɗu, ciki har da mambobi biyu na jam’iyya mai mulki ta Bangladesh National Party (BNP), sun mutu sakamakon rikicin siyasa a cikin makon da ya gabata.
Baya ga gidaje da aka ƙone ko aka lalata, an kuma banka wa wani ofishin ‘yan sanda wuta a garin Gopalganj, mahaifar Sheikh Hasina.
Jam’iyyarta ta Awami League, wadda yanzu aka haramta, ta kira a gudanar da yajin aiki a wannan makon domin tunawa da cikar shekara guda da yanke mata hukunci.
'Mijina ya riƙa gayyatar maza suna mini fyaɗe tsawon shekara 13'
Asalin hoton, Reuters
Lokacin da Joanne Young ta farka a ɗaure a kan gadonta, ba ta san irin mummunan lamaran da ya auku ba yayin da take sume.
Bayan ta ji mijinta Philip Young, wanda a wancan lokacin yake kira ga wani ya "sauka", sai ta fahimci cewa wani yana cikin ɗakin kwanansu.
Ba tare da sanin Joanne ba, Young ya yi talla a yanar gizo ga wasu maza su ci zarafinta. Daga nan sai ya bata ƙwaya mai gusar da hankali, sannan ya gayyaci wasu baƙi zuwa ɗakin kwanansu don su yi lalata da ita.
An kai hari kan jirgin dakon man fetur na biyu a gabashin mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa na Birtaniya ta sanar da cewa an kai hari kan wani jirgin dakon man fetur na biyu a kusa da mashigin ruwa na Hormuz.
A cewar rahoton, an kai wa jirgin, wanda ba a bayyana sunansa ba, hari da wani harbin makami da ba a tantance ko daga ina ya fito ba, inda ya bugi sashen ɗakin injin jirgin.
Hukumar ta ce jirgin na kan hanyarsa ta fita daga mashigin Hormuz ne lokacin da lamarin ya faru, kimanin kilomita 31 gabashin yankin Khasab na ƙasar Oman.
Ba a samu rahoton jikkata ko rasa rai sakamakon harin ba.
Tun da farko ma, an kai hari kan wani jirgin dakon man fetur a wata unguwa da ke kimanin kilomita 20 arewacin Khasab.
Putin mai kisan gilla ne kuma maƙiyin Ukraine - Zelensky
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi watsi da yadda Donald Trump ya bayyana shugaban Rasha, Vladimir Putin, a matsayin abokinsa.
Mista Zelensky ya bayyana wa tashar talabijin ta Amurka cewa shugaban na Rasha mai kisan rai ne kuma maƙiyin al’ummar Ukraine. A wani taro da aka gudanar a ƙasar Sin ranar Alhamis, Mista Trump ya yi takama da kyakkyawar dangantakarsa da Mista Putin, yana mai cewa kusancinsu yana ƙara wa Amurka tsaro.
Har ila yau, Mista Trump ya nuna takaicinsa kan tsananin gaba da ke tsakanin shugabannin Ukraine da Rasha, wanda ya ce ya sa tattaunawar samar da zaman lafiya ta kasance mai wahalar cimmawa.
A daren jiya kuwa, Rasha ta kai wani hari da ake zargin na “double tap” ne a birnin Kryvyi Rih, mahaifar Mista Zelensky. Wannan nau’in hari yana nufin kai hari na farko, sannan a sake kai wani yayin da masu aikin ceto da agaji suka isa wurin.
Mutane biyu sun mutu sakamakon harin, ciki har da wani jami’in bayar da agajin gaggawa da ke taimakawa bayan harin farko. Haka kuma, mutane da dama sun jikkata.
Rasha ta ƙaddamar da hare-hare a mahaifar shugaban Ukraine Zelensky
Rasha ta kai wasu hare-hare guda biyu a jere a tsakiyar binin Kryvyi Rih na Ukraine, mahaifar Shugaban ƙasar, Volodymyr Zelensky.
Mutum biyu ne suka rasa rayukansu, ciki har da wani yaro ɗan shekara bakwai da kuma wani ma'aikacin agajin gaggawa, wanda ya garzaya wurin bayan harin farko da aka kai da makamai masu linzami.
Wakiliyar BBC ta ruwaito jami'ai na cewa ce aƙalla mutum arba'in sun jikkata yayin da kafofin yaɗa labarai na yankin suka bayyana cewa wani gidan abinci da asibiti, da wasu gidajen zama sun lalace sakamakon hare-haren.
Tun da farko a jiya Juma'a, Ukraine ta fuskanci abin da Shugaba Zelensky ya bayyana a matsayin daya daga cikin manyan hare-haren da Rasha ta kai tun bayan fara yakin, inda har wasu makamai masu linzami da Rashar ta harba suka kai ga fadawa cikin Poland.
Trump ya yi barazanar hana Amurkawa gina cibiyoyin AI a ƙasashen waje
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar haramta wa kamfanonin Amurka gina cibiyoyin bayanai na fasahar AI a ƙasashen waje.
A wani taron manema labarai bayan dawowarsa daga Asiya, Mista Trump ya bayyana cewa kamfanonin za su fuskanci hukunci mai tsanani matukar suka dauki matakin hakan.
Ya ce "ba za mu bar cibiyoyin bayanai su tafi wasu kasashe ba, saboda China za ta kwashe su duka, kuma ba za mu bar haka ya faru ba, za mu kakaba haraji mai nauyi kan duk kamfanin da ya nemi ya yi haka."
Mista Trump ya nuna cewa bai riga ya tattauna batun da jami'an gwamnatinsa ba, kuma ba a sani ba ko matakin zai zama doka ba. Kamfanonin Amurka irin su Meta da Anthropic dai na daga cikin wadanda ke shirin kafa cibiyoyin a kasashen waje.
Ba za mu buɗe mashigar Hormuz ba sai an cika mana sharuɗɗa bakwai - Iran
Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce Iran ba za kwashe tare da fitar da sinadarin Uranium daga ƙasar ba, amma akwai yiwuwar samun mafita kan taƙaddamar.
A wata hira da ya yi da jaridar gwamnatin Iran, lokacin da aka tambaye shi game da makomar kusan kilogram 400 na uranium da aka tace zuwa kaso 60 cikin ɗari, ya ce: “Ina ganin za a iya samun wata dabara da za ta warware wannan matsala.”
Araqchi ya jaddada cewa Iran na da matsaya biyu da ba za su bari a tsallaka ba: kada a fitar da kayan nukiliyar daga cikin ƙasar, da kuma amfani da uranium ɗin bisa ga bukatun Iran.
A cewarsa, masu shiga tsakani sun gabatar da wasu shawarwari daban-daban, kuma akwai wasu daga cikinsu da za a iya la’akari da su. Ya ƙara da cewa ba za a iya ware batun uranium daga sauran rikice-rikicen da ake tattaunawa a kansu ba, domin dole ne a yanke shawara a cikin cikakken ƙunshin yarjejeniya.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce buƙatar farko ta Tehran ita ce shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili ya bayyana cewa yana son a cimma yarjejeniya, sannan Amurka ta ɗauki matakan amincewa domin Iran ta gamsu cewa Washington da gaske take wajen tattaunawar.
Ya jaddada cewa shirin kwana biyu na Iran na sake buɗe mashigin ruwa na Hormuz tare da fara tattaunawa har yanzu yana nan. A ƙarƙashin wannan shiri, Amurka za ta fara aiwatar da alƙawurran da Iran ke buƙata, sannan a ranar da ta biyo baya Tehran za ta buɗe mashigin Hormuz kuma za a iya fara tattaunawa.
Araqchi ya ce Iran na da sassauci dangane da lokacin aiwatar da shirin, amma dole ne a cika sharuɗɗa bakwai na Tehran kafin a bude mashigin Hormuz.
Ya kuma ce musayar sakonni tsakanin Iran da Amurka na ci gaba ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar da Pakistan, kuma Tehran na fatan cimma yarjejeniya da za ta hana sake barkewar yaki.
A gefe guda kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya ce a wani taron manema labarai da aka gudanar a Fadar White House ranar Juma’a cewa Iran na son yarjejeniya, amma ba ta shirya ta amince da yarjejeniyar da shi ke ganin za ta dace ba.
Ya ƙara da cewa: “Muna son yarjejeniya ta hakika, ba yarjejeniya ta bogi ba.”
Farawa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar daga nan sashen Hausa na BBC.
Za ku iya leƙwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta sauran labaranmu da kallon bidiyo, tare da tafka muhawara.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.