Abin da ya kamata ku sani kan bashin gidaje na gwamnatin Najeriya

Shugaba Tinubu
    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist Team Manager
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A baya-bayan nan ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar cewa ƴan Najeriya da suka cancanta za su iya samun bashin gidaje na kusan naira miliyan 100

Hakan na zuwa ne yayin da Najeriya ke fama da matsalar giɓin gidaje da ya kai miliyan 15 idan aka kwatanta da yawan al’ummarta

Shugaba Tinubu ya yi sanarwar ne a shafinsa na X inda ya ce an tsara shirin domin faɗaɗa hanyoyin samun gidaje da kuma sauƙaƙa damar mallakarsu a tsakanin ƴan Najeriya.

A Najeriya samun muhalli ya zama babban kalubale ga al’ummar kasar masu karamin karfi, inda kayan gini suka yi tsada sannan shirye-shiryen gwamnati sun gaza wajen samar da gidaje masu saukin kudi.

Yawancin gidajen da gwamnati da manyan ‘yan kasuwa ke samarwa sun fi karfin al’umma.

Tun bayan zuwan gwamnatin Shugaba Tinubu wasu matakan da ya dauka a bangaren tattalin arziki sun ta’azzara tashin farashi kaya a kowane bangare.

Amma a baya-bayan nan shugaban ya rika sanar da wasu shirye-shirye da sunan samar wa al’ummar kasar sauki, sai dai masana da dama na alakanta hakan da siyasa gabanin babban zaben kasar na 2027.

Ga abubuwan da suka kamata ku sani game da lamunin na gidaje da gwamnatin ta sanar:

Tsarin bayar da bashin yana aiki ne a ƙarƙashin Asusun Zuba Jari na Gidaje, Mofi na naira tiriliyan ɗaya da ke samar da damar tara kuɗin mallakar gida na tsawon lokaci a kan kuɗi ruwa da aka ƙayyade kan kashi 9.75.

Waɗanda suka cancanci cin gajiyar tsarin suna buƙatar su yi kafin alƙalami na kashi 10 na darajar kuɗin gidan, yayin da mutum ke da damar ɗaukan tsawon shekara 20 yana biyan kuɗin gidan sannu a hankali.

Gwamnati dai ta bijiro da shirin ne domin taimaka wa ƴan Najeriyar da kai tsaye ba za su iya biyan kuɗin a lokaci guda ba.

Ta yaya ƴan Najeriya za su iya samun lamunin?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya yi misali da gida da darajarsa ta kai naira miliyan 10.

Ya ce masu son gidan za su biya kafin alƙalami na naira miliyan ɗaya sannan kuma duk wata su riƙa rage kuɗin ta hanyar biyan naira 85,400 har tsawon shekara 20.

A saƙon nasa, Shugaba Tinubu ya ce fiye da ƴan Najeriya 2,300 daga jihohi 27 ne suka samu damar mallakar gidaje da kuɗinsu ya kai naira biliyan 160 ta tsarin MREIF.

Duk da cewa ƴan Najeriya musamman ma'aikata na fuskantar ƙalubale babba wajen mallakar gidaje saboda tsadarsu, Shugaba Tinubu ya yi iƙirarin cewa an bijiro da tsarin don magance wahalhalun da ƴan ƙasar ke fuskanta wajen samun gidaje a farashi mai sauƙi da kuma tsarin biya na dogon lokaci.

Tinubu ya ƙara da cewa ƴan ƙasar da suka cancanta za su iya cin gajiya ba tare da duba inda suke zaune ko kuma matsayinsu a tsakanin al'umma.

Tinubu ya ce "ba sai kun san minista, gwamna ko wani a Fadar Shugaban ƙasa ba don nema da kuma cin gajiyar waɗannan damarmakin."

A cewarsa, an tsara shirye-shiryen ne ga ƴan Najeriyar da suka cika ƙa'idojin, a duk inda suke,".

Dama dai bankin bayar da lamuni na Federal Mortgage Bank yana bayar da rance ga masu sha'awar mallakar gidaje a kan naira miliyan 50 da ke zuwa da kuɗin ruwa na kashi 6 cikin 100.

Sai dai waɗanda suka karɓi kuɗi ta wannan bankin za su ɗauki tsawon shekaru 30 suna biyan jimullar kuɗin gidan a hankali.

Baya ga wannan, ƴan Najeriyar da ke tsarin asusun haɗaka na pensho na iya amfani da kashi 25 cikin 100 na kuɗin ritayarsu da aka tara na tsawon shekarun da suka shafe suna aiki domin biyan kafin alƙalami, amma ya danganta da ƙa'idojin da aka gindaya.

Suma masu aure suna iya neman bashin ta hanyar yin haɗaka da abokan zamansu da nufin ƙara ba su dama ta samun bashin mai gwaɓi.

Matsalar gidaje na ƙara munana a Najeriya - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Najeriya na fama da matsalar karancin gidaje da yanayin da ke sahun kasashen da lamarinsu ya fi muni a duniya.

Fiye da kashi biyu cikin uku na 'yan Najeriya na zaune ne a gidaje irin na marasa karfi gami da rashin abubuwan more rayuwa kamar yadda jami'ar MDD da ke sa ido kan samar da gidaje Leilani Farha ta bayyana.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato ta tana wadannan bayanai a Abuja babban birnin kasar, yayin da ta kawo karshen wata ziyara ta kwana 10 da ta yi a shekarar 2019 domin binciken yanayin gidaje a manyan biranen kasar.

Ms Farha ta ce "Al'amarin gidaje a Najeriya na cikin mummunan yanayi. Zai yi wahala tsare-tsaren da ake da su a yanzu su iya magance babbar bukatar gidaje da ake da ita

"Ana ci gaba da samun karuwar muhallan da ba su da tsari inda yanayin ke azabtar da mutane, kuma tabbas hakan na daga cikin mafi muni a duniya."

Ta kara da cewa wasu muhallan ba sa samun ingantaccen ruwan sha da bandakuna da kuma wajen zubar da shara - kuma da yawan mutane na cikin hadarin kamuwa da cututtuka saboda yadda suke rayuwa kusa da gurbataccen ruwan da ba ya tafiya inda kwayoyin cuta ke yaduwa.

Ana sa ran yawan al'ummar Najeriya zai nunka sau biyu zuwa miliyan 400 a tsakiyar karnin nan, kuma dama tuni kasar ce mafi yawan mutane a nahiyar Afirka.

Rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar ya tursasa wa mutum miliyan biyu tsere wa daga gidajensu, kuma hakan na kara munana lamarin rashin gidajen.

Ms Farha ta ce cin hanci da rashawa da ya shiga bangaren gidaje ya jawo ana ta gina gidaje na gani na fada da suka fi karfin mallakar mafi yawan 'yan Najeriya.

Ta kuma soki tsare-tsaren da ake da su a bangaren gidaje da ta ce ba su da kyau, da kuma yadda hukumomi ke amfani da karfi da wajen korar wasu al'ummu daga muhallansu, wadanda mafi yawa mata ne da yara.

Jami'ar ta MDD ta ce: "Ana bukatar gwamnatin tarayya ta ayyana dakatar da fitar da mutane da ake yi daga muhallansu, har sai an samar da isasshiyar mafita da take kan tsari, domin tabbatar da cewa fitar da mutane da ake yi ya yi daidai da dokar kasa da kasa kan hakkokin dan adam."