Real Mallorca 0-3 Real Madrid: Real ta ci gaba da jan ragamar teburin La Liga

An wallafa

Real Madrid ta bayar da tazarar maki 10 a teburin gasar La Liga, bayan da ta je ta doke Real Mallorca 3-0 ranar Litinin.

Minti 45 ba ci a fafatawar da aka yi a gidan Mallorca, daga baya Vinicius ya ci na farko a minti 10 da fara zagaye na biyu, bayan da ya samu kwallo ta hannun Karim Benzema.

Benzema wanda ya ci Paris St-Germain kwallo uku rigis a Champions League, shine ya kara biyu a ragar Mallorca, daya daga ciki a bugun fenariti.

Real Madrid ta bai wa Sevilla ta biyu a teburi tazarar maki 10, kuma saura wasa 10 a karkare wasannin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Abokan hamayyar Real Madrid wato Atletico Madrid tana ta ukun teburi da kuma Barcelona, wadda take ta hudu.

A wasan farko da suka kara a tsakaninsu a bana, Real Madrid ce ta yi nasara da ci 6-1 ranar 22 ga watan Satumbar 2021.

Wadanda suka ci wa Real Madrid kwallayen sun hada da Isco da Karim Benzema da ya ci biyu da kuma Marco Asensio wanda ya zura uku rigis a raga.

Real Mallorca ta ci kwallo daya ta hannun Lee Kang-In a minti na 25 da fara taka leda.

'Yan wasan da Carlo Ancelotti ya je da su Mallorca.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fuidias.

Masu tsaron baya: Carvajal, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco da kuma Camavinga.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Jović, Bale, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.