Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hazard ya dawo taka leda, bayan jinyar kwana 81
Real Madrid za ta karbi bakuncin Celta Vigo a wasan mako na 24 a gasar cin kofin La Liga da za su fafata ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Tuni kocin Real, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 19 da za su fauskanci fafatawar a gida, ciki har da Eden Hazard wanda ya yi doguwar jinya.
Hazard ya ji rauni ne a watan Nuwamba, bayan da ya karo da Thomas Meunier a gasar Champions League da suka fafata da Paris Saint-Germain.
Tun farko an dauka sai a karawa da Manchester City dan wasan mai shekara 29 zai dawo murza leda, sai gashi ya koma fili da wuri.
Wasu ma sun sa rana tun a wasan hamayya da Real ta kara da Atletico Madrid, Hazard ya kamata ya koma buga wasa.
Hazard bai buga wa Real wasa 16 ba a dukkan fafatawar da ta yi, bayan da wasu suka yi hasashen cewar karawa 10 ce ba zai buga ba.
Watakila Zidane ya sa dan kwallon na Belgium ya buga masa minti 30 ko fiye da haka a wasa da Celta Vigo.
Kocin ba zai takura dan kwallon ba, domin Real za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan zagaye na biyu a Champions League ranar 26 ga watan Fabrairu a Spaniya.
'Yan wasan Real da za su fuskanci Celta Vigo:
Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Toni Fuidias.
Masu tsaron baya: Carvajal da Militao da Ramos da Varane da Marcelo da kuma Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.
Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Jovic da kuma Vinicius Jr.