Barca ba ta da tsayayyun masu cin kwallo, bayan Memphis a bana

Asalin hoton, Barcelona FC
Kungiyar Barcelona ita ce kan gaba mai 'yan wasa daban-dadan da ke ci mata kwallaye a La Liga ta bana.
Kawo yanzu 'yan wasan Barcelona 15 ne suka ci mata kwallo a kakar bana a babbar gasar Sifaniya.
Barcelona mai kwantan wasa ta yi nasarar doke Elche 3-2 ranar Asabar a Camp Nou a wasan mako na 18 a La Liga.
Ranar Asabar matasan 'yan wasan Barcelona, Jutgla da kuma Gavi suka ci Elche kwallaye da hakan ya sa suka shiga jerin 15 da ke ci wa kungiyar Camp Nou kwallaye a kakar bana.
Hakan ne ya sa Barcelona ke mataki na bakwai a kan teburi da maki 27, bayan nasara a karawa bakwai da canjaras shida da shan kashi a wasa hudu.
Kungiyar ta Camp Nou ta ci kwallo 28 aka zura mata 21 a raga a wasannin La Liga na shekarar nan.
Jumulla kwallo 30 Barcelona ta zura a raga 28 a La Liga da biyu a Champions League a dukkan fafatawa 23 da ta yi kawo yanzu a bana, kakar da take kamfar cin kwallaye kenan.
Memphis Depay ne kan gaba a cin kwallaye a La Liga mai takwas a raga bayan wasannin mako na 17 da kwantan wasa.
Sevilla da Real Madrid ne keda 'yan wasa 13 daban-daban da suka ci mata kwallaye a bana.
Ko a nahiyar Turai, kungiyar Chelsea da Hoffenheim ne ke kan gaba da 'yan wasa 16 daban-daban da suka ci musu kwallaye.
Wadanda suka ci wa Barcelona kwallaye a bana:
- Memphis: kwallo 8
- Ansu Fati: kwallo 4
- Nico: kwallo 2
- Pique: kwallo 2
- Coutinho: kwallo 2
- Braithwaite: kwallo 2
- Sergi Roberto: kwallo 2
- Gavi: kwallo 1
- Agüero: kwallo 1
- Abde: kwallo 1
- Jutgla: kwallo 1
- Araujo: kwallo 1
- Frenkie de Jong: kwallo 1
- Busquets: kwallo 1
- Luuk de Jong: kwallo 1

























