Saura maki uku tsakanin City da Liverpool

Sergio Aguero
An wallafa

Manchester City ta yi nasarar doke Arsenal da ci 3-1 a wasan mako na 25 a gasar cin kofin Premier da suka kara a Ettihad a ranar Lahadi.

City ta ci kwallayen ne ta hannun Sergio Aguero wanda ya ci uku rigis, kuma karo na 10 da ya yi wannan bajintar a Premier, Alan Sherer ne ke kan gaba da 11 a tarihi.

Arsenal ta zare kwallo daya ta hannu Laurent Koscielny tun a minti na 11 da fara tamaula.

Da wannan sakamakon City ta koma ta biyu da tazarar maki uku tsakaninta da Liverpool ta daya a kan teburi mai maki 62.

Arsenal kuwa ta koma ta shida a teburi, bayan da United ta doke Leicester City a ranar Lahadi ta koma ta biyar da tazarar maki biyu tsakaninta da Chelsea ta hudu mai maki 50.

A ranar Litinin ne West Ham United da Liverpool suka tashi 1-1 a karshen wasan mako na 25 a gasar ta cin kofin Premier.