Nadal ba zai buga gasar Wimbledon ba

Rafael Nadal na fama da jinya a kakar wasannin bana
Bayanan hoto, Rafael Nadal na fama da jinya a kakar wasannin bana
An wallafa

Tsohon zakaran wasan kwallon tennis, Rafael Nadal, ba zai buga gasar Wimbledon ba sakamakon raunin da ya yi a hannunsa.

Nadal ya sanar da hakan ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook ranar Alhamis.

Dan wasan sai hakura ya yi da buga gasar French Open da aka yi a Faransa a cikin watan Mayu, sakamakon raunin da ya yi.

Raunin da ya yi a hannunsa shi ne na baya-bayan nan, bayan ciwon baya da kafada da kuma gwiwa da ya yi jinya.