Gwamnatin jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura

Asalin hoton, Katsina state govt
Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, daga dukkan ayyukan masarautar da wasu tafiye-tafiyen biyo bayan zargin cin zarafin da wata baƙuwa mai yawon buɗe ido ta yi a kansa.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu na jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar 24 ga Nuwamba, 2026, gwamnatin ta ce ta kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Sarkin.
Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayar da umarnin kafa kwamitin domin gudanar da bincike kan lamarin tare da ba gwamnati shawarwari kan matakin da ya kamata ta ɗauka.
Gwamnatin ta bayyana damuwa kan zargin cin zarafin mata da ake yi wa Sarkin, wanda ya bazu a kafafen sada zumunta.
Ta kuma tabbatar wa al'umma cewa za ta tabbatar da an yi adalci, tare da aiwatar da dukkan shawarwarin da sakamakon binciken kwamitin ya fito da su.
Gwamnatin ta buƙaci jama'a su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bin doka da oda, tare da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

























