Fifa: Nigeria ta koma ta 12 a Afirka

Duk shekara ne hukumar Fifa ke fitar da irin wannan mataki
Bayanan hoto, Duk shekara ne hukumar Fifa ke fitar da irin wannan mataki
An wallafa

Nigeria ta gusa sama zuwa mataki na 12 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka, sannan kuma ta 61 a duniya.

A jerin kasashen da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta fitar da suka fi iya murza leda a ranar Alhamis, ya nuna cewar har yanzu Super Eagles bata cikin goman farko a Afirka.

Nigeria wadda a watan Mayu ke matsayi na 67 a duniya ta samu gusawa sama ne bayan da ta ci Mali da Luxembourg a wasannin sada zumunta da suka yi.

Algeria ce ta ci gaba da zama a matsayinta na daya a Afirka, yayin da Argentina ke kan gaba a duniya wajen iya taka leda.

Kasashen da ke biye da Algeria a cikin goman farko da suka fi iya taka-leda a Afirka sun hada da Cote d’ivoire da Ghana da Senegal da Masar da Tunisia da tsibirin Cape Verde da Jamhuriyar Congo da Guinea da kuma Kamaru.