'Ina iya gane mutumin da ke da aljanu ko maita da zarar mun haɗa ido'

Ruƙiyya na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake bi wajen cire aljanu da maita inda ake karanta ayoyin Alƙur'ani a kan ruwa kafin ya yayyafa wa majinyaci.
Bayanan hoto, Ruƙiyya na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake bi wajen cire aljanu da maita inda ake karanta ayoyin Alƙur'ani a kan ruwa kafin ya yayyafa wa majinyaci.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Tsawon shekaru, mutane daga al'ummomi daban-daban na tafiya wajen Mansur Ismail, wani malami mai ruƙiyya da ya shahara wajen yin maganin cututtukan da wasu ke ganin suna da alaƙa da shafar aljanu, ko maita ko wasu matsalolin da suka shafi maita, da fatan samun sauƙi.

Ruƙiyya wata hanya ce ta neman kariya da waraka a Musulunci, wadda ake amfani da karanta ayoyin Alƙur'ani da addu'o'i domin neman kariya, waraka da sauƙi daga cutarwar da ake ganin tana da alaƙa da aljanu.

Wannan al'ada ta daɗe a Najeriya, inda wasu mutane ke da imanin cewa aljanu na iya shafar mutum.

Mansur, wanda yake zaune a ƙaramar hukumar Makarfi da ke jihar Kaduna, ya ce ya fara wannan aiki ne daga gidansu.

A cewarsa, "Mutane da dama daga sassan Najeriya da ma wasu ƙasashe na zuwa wajena domin neman magani daga cutukan da suka yi imanin cewa ta aljanu ce."

BBC Pidgin ta tattauna da shi kan yadda yake gudanar da ruƙiyya ga mutanen da ke zuwa neman magani

Yadda Isma'il ya fara aikin ruƙiyya

Dis na di first step wia di healer dey summon di evil spirit wey possess di bodi of di patient.

Mansur ya ce ya fara aikin ne tun lokacin yana almajirci a Arewacin Najeriya, inda ya sha ganin yadda mahaifinsa ke taimaka wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali, lamarin da ya zaburar da shi ya ci gaba da wannan aiki.

Ya ce: "Babban dalilin da ya sa na zaɓi wannan aiki shi ne yadda na taso a gidan almajirai, inda nake kallon irin ayyukan da mahaifina yake yi."

"Mutane kan kawo marasa lafiya waɗanda halin da suke ciki ya tsananta sosai, har ta kai idan na kalle su, zan fahimci cewa suna fama da matsala mai tsanani."

"Ta hanyar taimakon da nake ba su, da kuma yardar Allah, mutane kan warke."

Ya ce ganin yadda mutane ke samun sauƙi bayan jinyar da yake yi musu, sannan su dawo cikin ƙoshin lafiya suna nuna godiyarsu, ya yi tasiri sosai a kansa, kuma hakan ne ya ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da aikin.

Oga Ismail

Ya kuma ƙara da cewa hanyarsa ta ruƙiyya ta haɗa da kula da mutanen da ke danganta matsalolin da suke da alaƙa da maita.

Ya ce: "Akwai wasu mutane da ke yin maita, kuma suke amfani da ita wajen cutar da sauran al'ummar da suke rayuwa tare."

A cewarsa, ta hanyar ruƙiyyar da yake yi, yana iya gano matsalolin da suka shafi aljanu ko waɗanda yake dangantawa da maita, tare da neman magance su ta hanyar karatun Alƙur'ani.

Ya ce: "Abin da ya bambanta ruƙiyyarmu da ta wasu shi ne, da farko, idan maita ta shafi mutum, muna da wata hanya ta musamman da muke bi wajen kula da shi, ta hanyar baiwar da Allah ya ba mu.

"Ka san ba duk wanda yake yin ruƙiyya ne zai iya yin hakan ba. A iya sanina, mutanen da Allah ya hore wa wannan ilimi ne kawai za su iya yin hakan."

Zarge-zargen da suka shafi maita da matsalolin shafar aljanu dai batutuwa ne da suka shafi imani na addini, kuma ba a tabbatar da su ta fuskar kimiyya ba.

One patient during di time wey di healer dey perform Ruqiyya

A cewarsa, mutane da dama na zuwa wajensa cikin mawuyacin hali, inda wasu ke fama da matsalolin da ke jefa su cikin tsananin rashin lafiya.

Ya ce a wasu lokuta, majinyatan kan shaida musu cewa suna fama da ciwon kai, fargaba da kuma yawan yin mafarkai masu tayar da hankali.

Ya bayyana cewa idan suka yi imanin aljani ne ya shafi majinyaci, sukan yi amfani da ayoyin Alƙur'ani wajen ƙoƙarin fitar da shi daga jikinsa.

Ya ce: "Idan aka kawo mana mutum da matsalar da ta shafi aljanu, muna amfani da Alƙur'ani da ayoyinsa wajen fitar da aljanin."

Ya ƙara da cewa ko da a yanayin da ba sa ganin aljani ne ya haddasa rashin lafiyar mutum, suna amfani da ayoyin Alƙur'ani a matsayin addu'ar neman waraka.

Ya ce: "Saboda ikon da Allah ya sanya a cikin Alƙur'ani, muna amfani da ayoyin da Allah ya saukar a cikinsa wajen yi wa majinyaci addu'a da roƙon Allah ya yaye masa wahalhalun da yake ciki."

Malamin ya ce imanin da yake da shi kan wannan aiki ya samo asali ne daga koyarwar addinin Musulunci.

Ya ce: "Ruƙiyya tana da matsayi da karɓuwa a Musulunci, kuma addinin ya tanadi hanyoyin gudanar da ita.

"Kowane Musulmi yana da imani da Alƙur'ani.

"Kuma duk wata cuta da Allah ya saukar, yana da maganinta a cikin Alƙur'ani."

Da aka tambaye shi yadda yake tantance ko maganin ruƙiyya ya yi tasiri, Isma'il ya ce masu gudanar da ruƙiyyar kan lura da sauye-sauyen da aka samu a yanayin majinyaci.

Ya ce: "Bayan mun kammala dukkan matakan ruƙiyya, abu na farko da muke yi shi ne ba wa majinyacin damar yin tafiya."

Ya ƙara da cewa sukan tambayi majinyacin ko har yanzu yana jin wani ciwo ko rashin jin daɗi a jikinsa.

Ya ce: "Idan mutum ya ce ba ya jin wani ciwo a ko'ina a jikinsa, wannan shi ne alamar farko da ke nuna mana cewa aljanin ya fita daga jikinsa, kuma duk wata maita da ta shafe shi ta gushe."

Wasu bidiyoyin ruƙiyya sun nuna yadda mutane da dama ke riƙe da majinyaci yayin da ake gudanar da jinyar.

Isma'il ya ce ana yin hakan ne domin kare lafiyar majinyacin.

Ya ce: "Muna riƙe da majinyacin ne saboda idan muka sake shi, aljanin da ke jikinsa na iya cutar da shi."

Ya ƙara da cewa: "Idan ana karanta Alƙur'ani tare da yayyafa ruwan da aka karanta masa ayoyinsa a jikin wanda aljani ya shafa, aljanin yana shan wahala. Kamar ana yayyafa masa wuta ne."

Ya ce wasu majinyatan kan yi ta kokawa sosai yayin zaman ruƙiyyar, kuma za su iya ji wa kansu rauni idan babu wanda ya riƙe su.

Ya ce: "Idan muka riƙe mutum, hakan yana ba mu damar gudanar da jinyar yadda ya kamata kuma cikin aminci."

Da aka tambaye shi yadda yake gane cewa majinyaci na buƙatar kulawar likitoci da ta wuce irin aikin da yake yi, Isma'il ya ce ruƙiyya ta fi mayar da hankali kan magance matsalolin da suka shafi aljanu, kuma akwai wasu yanayi da ba ya iya kula da su.

Ya ce: "Akwai mutanen da ke zuwa mana da wasu matsaloli da ake ganin suna da alaƙa da aikinmu, amma bayan mun duba halin da suke ciki, sai mu fahimci cewa ba za mu iya kula da su ba, don haka ba ma yi musu magani.

"Misali, mutum na iya buƙatar ƙarin ruwa a jikinsa ko kuma ƙarin jini."

Ya ce a irin waɗannan lokutan, sukan tura majinyatan zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Ya ƙara da cewa: "Idan matsalar ta wuce iyakar aikin da muke yi, kai tsaye muke tura mutum asibiti."

"Na zo ne saboda ciwon kai da mafarkai masu ban tsoro"

Wata mata mai suna Rayya Ashiru, wadda ta je neman magani a wajen Mansur, ta ce ta fara zuwa ne saboda yawan ciwon kai, firgici da kuma mafarkai masu tayar da hankali da take yi akai-akai.

Ta ce: "Na zo ne saboda ciwon kai, yawan firgici da kuma mafarkai masu ban tsoro da nake yi.

"Amma yanzu Alhamdulillah, ba na jin firgici, ciwon kai ko kuma yin waɗannan mafarkai."

Matar ta ce da farko ta fara zargin cewa wani ne ya yi mata illa ta hanyar tsafi, don haka ta yanke shawarar neman taimako domin gano abin da ke faruwa.

Ta ce bayan an yi mata magani tare da ci gaba da shan magunguna, ta samu sauƙi sosai.

Ta ce: "An yi mini magani, kuma yanzu jikina ya koma yadda yake a da.

"Saboda maganin da aka yi mini, na samu sauƙi sosai."

Mene ne matsayin ruƙiyya a addinin Musulunci?

Ruƙiyya wata hanya ce ta neman kariya da waraka a Musulunci, wadda ta ƙunshi karanta ayoyin Alƙur'ani da addu'o'in Annabi domin neman kariya, waraka da sauƙi daga cutarwar da ake dangantawa da al'amuran aljanu.

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Mustapha Umar, da ke jihar Sakkwato, ya shaida wa BBC Pidgin cewa yin ruƙiyya ya halatta a Musulunci, muddin ana gudanar da ita ta hanyar karatun Alƙur'ani.

Ya ce: "Ruƙiyyar da ake yi ta hanyar karanta Alƙur'ani ta halatta a Musulunci, matuƙar ba a aikata wani abu da addini bai yarda da shi ba.

"Mutum na iya amfani da karatun Alƙur'ani wajen fitar da aljanin da ya shafi wani."

Da aka tambaye shi game da ruwan da aka ga malamin yana zubawa a jikin mutumin da ake zargin aljani ya shafa, ya ce:

"Idan ayoyin Alƙur'ani aka karanta a kan ruwan da ake zubawa a jikin mutumin da aljani ya shafa, babu laifi. Amma idan aka aikata wani abu da ya saɓa wa koyarwar Musulunci, to ruƙiyyar ta sauya zuwa wani abu daban, kuma ba ta halatta a Musulunci ba."