Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 23/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 23/11/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • INEC
  • Atiku
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Yan Houthi a Yemen sun ce an kashe mutum 10 a hare-hare ta sama

    Kafofin yaɗa labaran da ke da alaƙa da 'yan tawayen Houthi na Yemen sun ce an kashe mutum 10 a hare-hare ta sama da kawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta suka kai birnin tashar jiragen ruwa na Hodeidah.

    'Yan Houthi, waɗanda Iran ke marawa baya kuma suke iko da manyan sassan Yemen, ciki har da birnin Hodeidah, na yaƙi da dakarun gwamnatin Yemen da Saudiyya ke goyon baya.

    Gwamnatin Saudiyya ba ta ce komai ba kan harin kawo yanzu.

    Yemen na fama da yaƙin basasa sama da shekaru goma.

    Yaƙin da ake yi a ƙasar a halin yanzu ya samo asali ne a watan Yulin wannan shekara, bayan da kawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya kai hari kan filin jirgin saman birnin Sanaa, babban birnin Yemen, domin hana wani jirgin saman Iran sauka a filin.

  2. Ban ga dalilin kai wa Iran harin soji ba – Eisenkot

    Eisenkot

    Gadi Eisenkot, wanda ke tattaunawa kan kafa sabuwar gwamnati a Isra'ila, ya ce bai ga dalilin da zai sa a kai wa Iran harin soji ba.

    Tsohon babban hafsan hafsoshin sojin Isra'ila, wanda ke fatan zama firaministan ƙasar, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a majalisar dokokin Isra'ila (Knesset) da ke birnin Jerusalem.

    Ya ce: "Barazanar Iran ita ce mafi muni da ke fuskantar gwamnatin Isra'ila, amma a halin yanzu, ban ga wata barazana kai tsaye kuma ta gaggawa da ke bukatar ɗaukar mataki kafin a kafa sabuwar gwamnati ba."

    Sai dai Benjamin Netanyahu, wanda har yanzu yake riƙe da muƙamin firaminista bayan zaɓen Isra'ila, ya yi gargaɗi kan "manyan barazanar da ke fuskantar Isra'ila", da kuma haɗarin raina girman barazanar.

  3. An dawo da Jensen Huang a matsayin shugaban kamfanin Nvidia

    Nvidia

    Hukumar gudanarwar kamfanin fasahar zamani na Nvidia ta amince da sake naɗa Jensen Huang a matsayin shugaban kamfanin, tana mai cewa shi ne mutumin da ya dace ya jagorance shi.

    A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet, shugabanta ya ce dukkan mambobin hukumar sun amince da matakin, yana mai cewa dawo da Huang kan muƙaminsa shi ne abin da ya fi dacewa da masu hannun jari, ma'aikata, abokan hulɗa da kwastomomin kamfanin.

    Bayan wannan mataki, Huang ya bayyana farin cikinsa da karramawar na sake jagorantar Nvidia, yana mai cewa kamfanin na cikin manyan cibiyoyin fasaha mafi muhimmanci a duniya, a daidai lokacin da ake tunkarar wani sabon sauyi a masana'antu.

    A cikin sanarwar tasa, Huang ya ce ya karɓi muƙamin cikin girmamawa, tare da aniyarsa ta ci gaba da jagorantar kamfanin.

    Ya kuma gode wa hukumar gudanarwar kamfanin bisa amincewar da ta nuna masa, musamman shugabanta Harvey Jones bisa jagorancinsa, da kuma Colette Kress tare da sauran manyan shugabannin kamfanin bisa yadda suka tafiyar da Nvidia a lokacin.

  4. An zaɓi filayen wasa shida don buga gasar Afcon 2027

    Filin wasa

    Kasashe uku da za su karɓi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON ta shekarar 2027, Kenya da Tanzania da kuma Uganda, sun zaɓi filayen wasa shida da za a gudanar da wasannin gasar.

    An sanar da filayen wasan ne a yayin taron Hukumar Kwallon Kafar Afirka (CAF) da aka gudanar a Najeriya a ƙarshen makon jiya.

    A birnin Nairobi, za a buga wasu daga cikin wasannin gasar a sabon filin wasa na Talanta Stadium mai ɗaukar mutane 60,000, wanda ake sa ran za a buɗe shi a watan Janairu.

    Ita kuwa Tanzania, za ta karɓi bakuncin wasanni a filayen wasa uku da ke biranen Arusha da Dar es Salaam da kuma Zanzibar.

    A Uganda, za a yi amfani da Mandela National Stadium da ke Kampala, da kuma sabon filin wasa na Hoima City Stadium, wanda ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar ke amfani da shi a wasanninta na ƙasa da ƙasa na baya-bayan nan.

    Har yanzu ba a tantance filin wasan da za a buga wasan ƙarshe na gasar ba, wadda ƙungiyoyi 24 za su fafata a cikinta daga ranar 19 ga Yuni zuwa 17 ga Yuli.

    A gasar AFCON ta baya da aka yi a Moroko tsakanin Disambar 2025 da Janairun 2026, an gudanar da wasannin ne a filayen wasa tara da ke cikin birane shida na ƙasar.

  5. Lebanon ta yi Allah wadai da ziyarar wata ƴar Isra'ila zuwa makarantun ƙasar

    Jami’ai a Lebanon sun yi Allah-wadai da ziyarar da wata mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ta kai wata makaranta da ke yankin da mabiya adadinin Kirista ke zaune a kudancin Lebanon inda Isra’ila ta mamaye.

    Ella Waweya mai magana da Larabci ta wallafa wani bidiyo da ya nuna ta a tsaye jikin wani aji 'cike da yara a wata makaranta da ke ƙauyen Debl.

    Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya zargi Isra’ila da amfani da 'ɗalibai wajen yaɗa farfaganda.

    Ƙauyen Debl na cikin wasu ƙauyuka da ke kusa da iyakar ƙasashen biyu, waɗanda mafi yawan mazaunansu Kiristoci ne.

    Yawancin mazauna ƙauyukan sun ƙi barin gidajensu duk da umarnin sojin Isra’ila suka basu na barin yankin.

    An wallafa bidiyon ya yin da Lebanon ke bikin ranar samun 'yancin kai. break

  6. Bangladesh ta ce za ta kama Sheikh Hasina idan ta koma ƙasar

    ..

    Bangladesh ta ce za a kama tsohuwar Firaministar ƙasar, Sheikh Hasina tare da tsare ta a gidan yari idan ta dawo daga gudun hijirar da ta ke yi a Indiya.

    Shaekarar da ta gabata, wata kotu ta musamman ta yanke mata hukuncin kisa sakamakon samunta da hannu a kashe mutane ya yin zanga-zangar da ta gudana shekaru biyu da suka gabata, wadda ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatinta.

    Ƙaramar ministar harkokin wajen ƙasar, Shama Obaed, ta buƙaci Indiya ta mutunta yarjejeniyar musayar mutanen da ake nema ruwa a jallo tsakanin ƙasashen biyu, tare da miƙa mata Sheikh Hasina a matsayin wadda aka samu da laifi.

    Hasina ta nemi Babban Ofishin Jakadancin Bangladesh da ke Indiya da ya ba ta fasfo domin ta koma Dhaka a watan Disamba.

    A nata ɓangaren, Indiya ta ce tana nazarin buƙatar Bangladesh na a miƙa mata tsohuwar firaiministar.

  7. Koriya da Kudu ta ce sojojinta ba su da niyyar shiga yaƙin Iran

    Ministan Tsaron Koriya ta Kudu ya ce faɗaɗa aikin yaƙi da masu fashin teku a yankin Tekun Aden ba yana nufin ƙasarsa za ta shiga yiwuwar yaƙin da Amurka da Isra'ila za su yi da Iran ba.

    Kang Shin-chul ya shaida wa majalisar dokokin Koriya ta Kudu cewa sojojin da aka tura yankin ba za su shiga ko wace irin ayyukan soja kai tsaye ko a kaikaice da ke da alaƙa da rikicin mashigar ruwa ta Hormuz ba.

    A cewarsa, hare-haren masu fashin teku a yankin sun ninka har sau uku cikin shekara guda da ta gabata, kuma manufar wannan aiki ita ce kare jiragen ruwan Koriya ta Kudu da kuma 'yan ƙasar da ke amfani da wannan hanyar ruwa wajen zirga-zirga.

  8. Ukraine ta tabbatar da hari kan jirgin yaƙin Rasha a tekun Libya

    Zelensky

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce jiragen ruwa marasa matuƙa na rundunar sojin ruwan ƙasarsa sun nutse da wani jirgin yaƙin Rasha a tekun gaɓar Libya a ranar Lahadi.

    A cewar ikirarin jami'an Ukraine, harin ya kuma yi wa wani jirgin dakon kaya na Rasha da ake amfani da shi wajen jigilar makamai fintinkau.

    Da safiyar Lahadi, gwamnatin da ke iko da gabashin Libya ta ce wani fashewa ya auku a cikin jirgin yaƙin yayin da yake ajiye a tashar jiragen ruwa ta Benghazi domin ɗaukar man fetur da sauran kayayyaki kafin ya koma Rasha.

    A wani ɓangaren kuma, Ma'aikatar Lafiya ta Libya ta ce ta karɓi wasu da suka jikkata daga wani jirgin kasuwanci da aka kai wa hari a kusa da tashar jiragen ruwan.

    Sai dai ba a bayyana ko wannan ne jirgin da Ukraine ta ce ta kai wa hari ba.

    Ya zuwa yanzu, Moscow ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Zelensky ya yaba da abin da ya kira "gagarumar nasarar aikin" da Ukraine ta aiwatar a matsayin martani ga abin da ya bayyana a matsayin hare-haren Rasha.

    Zelensky ya ce an yi amfani da jiragen ruwa marasa matuƙa guda bakwai wajen kai hari da kuma nutsar da Corvette Merkury, wanda ya ce na ɗaya daga cikin sabbin jiragen yaƙin Rasha.

    Ya ƙara da cewa an kuma lalata wani jirgin sama mai saukar ungulu na soji kirar Ka-27.

    Shugaban na Ukraine ya kuma ce jirgin ruwa na biyu da aka kai wa hari shi ne MV Angara, wani jirgin dakon kaya na Rasha.

  9. Za mu yi duk mai yiwuwa don tunkarar takunkuman Amurka - Iran

    ...

    Iran ta ce ba za ta amince da ci gaba da takunkumin Amurka da ƙaƙaba mata shingen tattalin arziki ba, kuma za ta yi amfani da duk hanyoyin da take da su domin tinkarar su.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, Esmail Baghaei, ya bayyana takunkumin da shingen tattalin arzikin da Amurka ke ƙaƙaba wa Iran a matsayin "wani nau'i na hare-haren yaƙi", yana mai cewa "Iran na da 'yancin amfani da duk wata hanya wajen kare kanta bisa tanadin Sashe na 51 na Kundin MDD."

    Mista Baghaei ya ƙara da cewa hukumomin Iran na nazarin "haɗakar matakan siyasa, diflomasiyya da na kariya" domin mayar da martani ga takunkuman, waɗanda za a aiwatar kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka ga dama.

    A jiya, yayin wata hira da kafar Fox News, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar nutsar da jiragen ruwan Iran lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar Iran ta yi ƙoƙarin karya shingen ruwa da aka kakaba mata.

    "Ina fatan su yi hakan. Za a aika da su ƙarƙashin teku kamar yadda aka yi da sauran rundunar ruwan Iran," in ji shi.

  10. INEC ta faɗi rumfunan da za ta yi gwajin zaɓen shugaban ƙasa

    INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fitar da jerin rumfunan zaɓen da ta zaɓa domin gudanar da gwajin zaɓen shugaban ƙasa da za ta gudanar ranar 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X ta ce a ranar za ta gudanar da gwajin abubuwa da dama da suka haɗa da tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma ɗora sakamakon zaɓe ta na'ura a faɗin ƙasar.

    Hukumar ta ce za a gudanar da wannan gwaji ne a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaɓa daga cikin mazaɓun ƙasar 8,838.

    INEC ta kuma wallafa rumfunan da ta zaɓa a shafinta na intanet domin masu ruwa da tsaki da kuma jama'a su gani.

    Hukumar zaɓen ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.

    “An tsara wannan gwaji ne domin auna yadda BVAS ke aiki, tantance hanyoyin tabbatar da masu zaɓe, da kuma gano duk wata matsalar fasaha da ka iya tasowa kafin babban zaɓen shekarar 2027'', a cewar INEC.

  11. Ina tsaka da yin aski aka ɗauke ruwa a Villa - Tinubu

    Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa ba talakawa ne kaɗai ke fuskantar matsaloli ba a ƙasar, har ma da shi kansa.

    Amma kuma ya ce yana da yaƙinin cewa ƙasar za ta fita daga cikinsu nan ba da jimawa ba.

    Yayin da yake jawabi a wurin taron addu'o'i da aka shirya masa a Legas, shugaban ƙasar ya ce matsalar ruwan sha ta kai har a fadarsa da ke Villa.

    ''A ranar Larabar makon da ya gabata ina tsaka da yin aski a Villa kwai sai aka ɗauke ruwa, don haka muma muna fuskantar waɗannan matsaloli'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ''ya kamata mu gyara waɗanann matsaloli na rashin wuta, rashin ruwa, rashin ayyukan ci gaba, kuma za mu gyara su ga Najeriya'', in ji shi.

  12. Ana shirin fara Gasar Karatun Qur'ani ta duniya a Pakistan

    Makaranci

    Shahararrun mahaddatan Alƙur’ani daga sassa daban-daban na duniya sun fara isa Pakistan domin halartar gasar karatun Alƙur’ani ta duniya.

    Ma’aikatar Harkokin Addini ta Pakistan ce ke shirya gasar, wadda za a gudanar a birnin Islamabad daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Nuwamba, tare da halartar mahaddata daga ƙasashe 32 ciki har da Pakistan.

    Mahaddata daga Kamaru da Togo da Mozambik da Uzbekistan sun isa Islamabad a daren Lahadi, yayin da mahalarta daga Jamus da Jordan da Aljeriya da Iraki da Libiya da Turkiyya suka isa ƙasar a ranar Litinin.

    Haka kuma, mahaddata daga Tunisiya da Côte d’Ivoire da Masar da Tanzaniya da Gambiya da Najeriya da Qatar da Moroko da Faransa sun isa Islamabad domin shiga taron na kwanaki uku.

    Fitaccen gwanin Alƙur’ani na duniya, Qari Syed Sadaqat Ali, ne zai kasance babban alƙalin gasar karatun Alƙur’anin ta ƙasa da ƙasa karo na biyu.

    Ana sa ran sauran mahaddatan daga ƙasashen da za su halarta za su ci gaba da isa Pakistan har zuwa daren Litinin.

  13. Tinubu ya umarci Masari ya sasanta da Dikko

    Masari

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bukaci babban mai ba shi shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Kabir Masari ya sasanta da gwamnan Katsina Umar Dikko Radda.

    Yayin da yake jawabi a wajen taron addu’o’i na musamman da ‘yan uwansa suka shirya masa a Yoruba Tennis Club da ke Legas, shugaba Tinubu ya ce shugabannin jam’iyyar APC su ajiye saɓanin ra’ayi a tsakaninsu, su yafe wa juna tare da rungumar sulhu yayin da jam’iyyar ke shirin babban zaɓen shekarar 2027.

    Bayanai na cewa akwai saɓanin siyasa tsakanin Masari da Gwamna Radda, lamarin da ya shafi tafiyar siyasar ɓangarorin biyu a jihar.

    A wata hira da BBC a baya-bayan nan Ibrahim Kabir Masari ya tabbatar da saɓani tsakaninsa da gwamnan, sai dai ya ce bai taɓa nadamar taimaka masa ba.

    Kan haka ne Shugaba Tinubu ya umarci Masarin ya koma gida domin sasanta duk wata matsala da ke tsakaninsu.

    “Ya kai abokina, sarkin aiki, Alhaji Kabiru Masari, ka koma gida ka sasanta kowa da kowa. Wannan umarnin shugaban ƙasa ne. Bayan ka kammala haka, sai ka je Jigawa da sauran wurare domin sulhunta mutane, ka roƙe su, domin dole ne mu sasanta, kuma duk wani fushi ya kau.”

    Haka kuma ya bai wa Abubakar Badaru, wanda tsohon gwamnan Jihar Jigawa ne, irin wannan aiki, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar.

    Tinubu ya ce bai kamata matsalolin ƙashin kai su yi wa muradun APC na bai ɗaya barazana ba, musamman yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin ci gaba da riƙe mulki a zaɓen shekarar 2027.

  14. Muna shirin daina ƙera jiragen yaƙi masu amfani da direbobi

    ;;;

    Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Birtaniya (RAF) ya ce jirgin yaƙi na zamani da ƙasar ke shirin ƙerawa nan gaba na iya kasancewa jirgin yaƙi na ƙarshe da matuƙi ke sarrafawa.

    Air Marshal Harvey Smith ya ce jiragen yaƙi marasa matuƙa da ke amfani da fasahar ƙirƙirar basira ta na’ura (AI) za su sauya fasalin harkokin jiragen yaƙi na soji gaba ɗaya.

    Jawaban nasa na da nasaba da shirin Global Combat Air, wani haɗin gwiwa tsakanin Birtaniya da Italiya da Japan na ƙera jirgin yaƙi, wanda ake sa ran zai fara aiki nan da shekarar 2035.

    Ana sa ran jirgin, wanda aka fi sani da Tempest, zai kasance mai saurin gaske, yana da fasahar ɓuya daga na’urorin gano jirage (stealth), da na’urorin sa ido na zamani, da kuma fasahar AI da za ta taimaka wa matuƙa wajen sarrafa yanayi mai cike da bayanai ko matsanancin matsi.

    A wani sharhi da ya rubuta a jaridar Telegraph, Harvey Smith ya ce jirgin yaƙin “na iya zama jirgin yaƙi na ƙarshe da matuƙi ke tukawa da za mu taɓa ƙerawa.”

    Ya ce hakan ba yana nufin rawar ɗan Adam na raguwa ba ne, sai dai ci gaban fasaha na sauya yadda ake gudanar da yaƙe-yaƙen sama.

    Harvey Smith ya ce a nan gaba, fasahar ƙirƙirar basira ta na’ura da kuma injuna ne za su riƙa gudanar da “ayyuka mafi haɗari ga ɗan Adam”, amma ya jaddada cewa ya kamata fasaha ta taimaka wa ɗan Adam wajen yin hukunci da yanke shawara, ba maye gurbinsa wajen ɗaukar alhaki ba.

    Shugaban rundunar sojin saman ta Birtaniya ya kuma ce: “Daga shekara mai zuwa jiragen yaƙi marasa matuƙa za su fara shawagi a sararin samaniyar Birtaniya. Wannan abu ne mai ƙayatarwa kuma wajibi.”

  15. Adadin waɗanda suka mutu a hatsarin kwale-kwalen Bayelsa ya kai 29

    Douye Diri

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen da ya auku ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Southern Ijaw da ke Jihar Bayelsa ya ƙaru zuwa mutum 29, yayin da sama da mutum 50 da suka tsira ke karɓar magani a asibitoci.

    Gwamnan jihar, Douye Diri, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar jaje da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai masa.

    Diri ya ce har yanzu ba za a iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu gaba ɗaya ba, domin ana ci gaba da ƙoƙarin ciro kwale-kwalen da ya haddasa hatsarin.

    Sai dai ya ce akwai yiwuwar wasu fasinjoji na nan maƙale a cikin kwale-kwalen.

    Gwamnan ya yi zargin cewa kwale-kwalen bai dace da zirga-zirgar ruwa ba, sannan kuma ya tashi ne daga wata tashar fasinjoji da ba a amince da ita ba.

  16. Birtaniya za ta fara amfani da AI domin gano cutar kansar mama

    Birtaniya za ta fara gwaji mafi girma a duniya da ke amfani da fasahar AI domin taimakawa wajen gano cutar kansar mama.

    Ana gayyatar mata kusan 700,000 domin su shiga wannan gwaji.

    Za a yi amfani da fasahar AI wajen duba sakamakon hotunan sassan jiki (X-ray), domin ganin ko za ta iya inganta gano cututtuka da wuri tare da rage nauyin aiki kan ma'aikatan kiwon lafiya.

    Farfesa Fiona Gilbert na daga cikin jagororin gwajin, wadda kuma ta ce suna da yaƙinin cewa fasahar za ta taimaka wurin inganta kaifin basirar ma'aikatan lafiya kuma za a iya gano masu cutar kansa da dama.

    Kansar mama na daga cikin cutuka mafiya yawa a tsakanin matan Birtaniya.

  17. Jirgin yaƙin Rasha ya fashe a tekun Libya

    ..

    Gwamnatin yankin Libya ta bayyana cewa an samu fashewa a cikin wani jirgin ruwan yaƙi na Rasha a birnin Benghazi.

    Ana zargin harin jirgi mara matuƙi ne aka kai kan jirgin ruwan, sannan ta ƙara da cewa daga baya an kai hari kan wani jirgin ruwan kasuwanci mai ɗauke da tutar Malta.

    Mutane goma ne suka jikkata sakamakon fashewar da ta faru a jirgin na Rasha, kuma jirgin ruwan mai suna Merkury—ya kusan nutsewa.

    Ba a bayyana ko su waye ke da alhakin kai hare-haren ba.

    Sai dai ana cewa ƙwararrun 'yan Ukraine masu sarrafa jiragen sama marasa matuƙa suna aiki a yammacin ƙasar Libya.

  18. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, Mande tushen aiki da ko da nasara na tsoronki kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.