Ancelotti ya juya wa AC Milan baya

Ancelotti ya taba jagorantar Chelsea
Bayanan hoto, Ancelotti ya taba jagorantar Chelsea
An wallafa

Carlo Ancelotti ya ki amincewa ya kara komawa AC Milan a matsayin kocin tawagar 'yan kwallon kulob.

A makon da ya gabata ne, Real Madrid ta sallami Ancelotti mai shekaru 55.

Ancelotti ya tattauna da shugaban Milan, Adriani Galliani a kan batun ya kara koma wa jan ragamar kungiyar, wacce a baya ya lashe gasar zakarun Turai tare da ita har sau biyu.

Milan ta kamalla kakar wasan da ta wuce a matsayin na 10 a kan tebur a karkashin jagorancin Filippo Inzaghi.

Ancelotti ya ce "Ina godiya ga AC Milan da ta nuna sha'awa a kai na. Amma ina bukatar hutu kuma ina yi wa kungiyar fatan alheri."