Jaaskelainen: Sabon kwantaragi

Jaaskelainen zai ci gaba da zama a West Ham zuwa shekarar 2015
Bayanan hoto, Jaaskelainen zai ci gaba da zama a West Ham zuwa shekarar 2015
An wallafa

Mai tsaron gidan West Ham Jussi Jaaskelainen ya sanya hannu kan sabon kwantiragin shekara daya da zai ba shi damar ci gaba da zama a kungiyar zuwa 2015.

Jaaskelainen mai shekaru 39, ya shiga kulob din West Ham a tsarin musayar 'yan wasan nan da ba biyan kudi, bayan ya kwashe shekaru 14 a Bolton inda ya yi wasanni 18 a gasar Premier a shekarar 2013-14.

Amma a karshen kakar, Andrian ya zama mai tsaron gida na farko da West Ham ta fara muradi bayan ajiye Jaaskelainen a watan Janairu.

Jussi ya bayyana a shafin sadarwa intanet na West Ham cewa, "ina jin dadin jikina kuma na ji dadi a kakar gasar da a ka kammala, ina kuma fatan dorawa daga inda na tsaya."