Cisse da Newcastle sun sasanta

papiss cisse
Bayanan hoto, Ba Papiss Cisse ba ne kadai musulmi a Newcastle amma shi kadai ne ya ce ba zai sa rigar ba
An wallafa

Papiss Cisse da Newcastle sun cimma matsaya da ke nufin dan wasan yanzu zai sa rigar wasan kungiyar da a da ya ce ba zai sa ba.

Cisse dan kasar Senegal a da ya ce ba zai sa rigar wasan kungiyar ba saboda tambarin kamfanin da ya dauki nauyinta mai suna Wonga mai bada bashi na ta'ammali da kudin ruwa.

Wanda shi kuma dan wasan ya ke ganin sanya rigar da ke zaman tallata kamfanin ya sabawa akidar addininsa.

Wannan dambarwa ta sa Cisse ya ki bin 'yan wasan kungiyar zuwa rangadin wasannin shirin tunkarar kakar wasanni mai zuwa.

Sai dai kuma bayan mako daya da a ka dauka ana tattaunawa tsakanin bangaren dan wasan da na kungiyar, yanzu Cissen ya yarda ya sa rigar.

A ranar Juma'a dan wasan mai shekaru 28 zai dawo cikin tawagar domin ci gaba da atisaye.

Bayan da ya kauracewa kungiyar da ta ke rangadin wasanni a Portugal.