Nigeria: An yi maci kan cin zarafin yara

An wallafa

Wasu masu fafutuka a Nigeria sun shirya wani maci da suka kira '' one million-man silent march'' a kan cin zarafin kananan yara.

An shirya macin ne, wanda wata kungiyar farar hula mai suna Playback Nigeria ta jagoranta, da nufin nuna adawa da karuwar cin zarafin kananan yara da ake yi a kasar.

Wadanda suka shirya macin dai sun ce an gudanar da shi a birane daban-daban na kasar, don fadakar da jama'a illar da ke tattare da cin zarafin kananan yara.

Wadansu suka yi macin dai sun rufe bakunansu don su nuna takaici da yadda al'umma ba ta cewa komai game da cin zarafin kananan yara a kasar.

Shugaban kungiyar Playback Nigeria, Damilola Akwetiyeri, ya ce, "Idan aka lura za a ga an yiwa yaran da ke wannan maci zane mai kama da ciwo--muna so ne mu nuna wa al'umma cewa lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen cin zarafin yara.

"Yawancin yara akan ci Zarafinsu ne a gida, ko a makaranta, ko ma a kan hanya; a kan kuma yi ta hanyar lalata da su.

"Lokaci ya yi da ya kamata a daina yin shiru a kan batun cin zarafin yara, muna so al'umma ta tashi mu hada karfi da karfe don magance wannan matsala".