Kenya: Ana fafutukar halatta auren jinsi daya

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Wata kungiyar masu fafutuka ta shigar da kara babbar kotun kasar Kenya, inda take bukatar a halatta auren jinsi.
Yanzu haka dai auren jinsi a Kenya mummuna laifi ne da ake yankewa duk wanda aka kama da laifin yin sa hukunci shekara 14 a gidan yari.
Hukumar kare hakkin dan adam da masu luwadi ta kasar, ta ce dokar ta keta hakkokin daidaito da martaba da kuma hakkin dan adam.
A shekarar da ta gabata ne mataimakin shugaban Kenya, William Ruto, ya ce su luwadi da madigo basu da wajen zama domin kasar ba ta maraba da su.






















