Ana binciken Facebook kan saba doka

Asalin hoton, Getty
An wallafa
Mahukunta a kasar Jamus na binciken shafin sada zumunta na Facebook kan karya dokoki a harkar sada zumunta.
Hukumomin kasar dai na zargin cewa shafin sada zumuntar ya karya dokar da ta shafi kariya na bayanai sirri ma su abota da shafin.
Binciken yana duba ko mamaye harkar shafin sada zumunta da Facebook ya yi na nufin ka'idojin da shafin ke shimfida wa ga masu mu'amala da shi sun saba wa doka.
Wannan shi ne bincike irin sa na farko da wani shafin sada zumunta ya taba fuskanta, sai dai Facebook ya ce yana da kwarin guiwar cewa bai karya wata doka ba.





















