Saudiyya ta gayyaci Najeriya shiga rundunar hadaka

Asalin hoton,
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ta samu goron gayyatar shiga kawancen sojojin kasashen musulmi daga Saudiyya. A hirarsa da BBC mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya ce sai dai har yanzu gwamnati ba ta yanke shawarar ko za ta shiga kawancen ba ko a'a. Sai dai ya ce kasar na goyon bayan kowane irin yunkuri na kawar da ta'addanci a duniya. A ranar Talata ne Saudiyya ta sanar da kafa wata sabuwar hadakar dakarun soji tsakanin kasashe 34 domin yaki da ta'addanci. Kamfanin dillancin labaran kasar SPA, ya ce daga birnin Riyadh na Saudiyya za a rika tsara ayyukan dakarun kawancen. Kasashen dake cikin hadakar, daga yankunan Larabawa, da Asiya ta Kudu da kuma Afirka suke. Hadakar dakarun za ta yaki kungiyoyin masu tsattsaurar akida a Iraqi, da Syria, da Libya da Masar da kuma Afghanistan. Sai dai babu cikakken bayani game da yadda hadakar za ta tunkari wannan yaki a zahiri. Kasashen larabawa na yankin Gulf dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba a kan su kara hobbasa wajen yaki da kungiyar IS a Iraqi da Syria






















