Zabiya sun shiga tasku a Najeriya

Mutum daya daga cikin su har ya mutu saboda rashin kulawa
Bayanan hoto, Mutum daya daga cikin su har ya mutu saboda rashin kulawa
An wallafa

Gidauniyar da ke fafutukar kare hakkin masu larurar zabiya a Najeriya ta koka da yadda babban asibitin kasar da ke Abuja ya dakatar da kula da lafiyarsu.

Asibitin dai ya sanar da dakatar da ba wa zabiya zabiya masu dauke da cutar daji wato Cancer magani lamarin da ya kai ga daya daga cikin marasa lafiyar ya rasa ransa.

An ce asibitin ya dauki wannan matakin ne na dakatar da kula da masu larurar zabiya din sakamakon bashin Naira miliyan 50 da asibitin ke bin gwamnatin Nigeria.

Cututtukan da suka shafi fatar jiki da cutar Cancer na daga cikin manyan cututtukan da suke addabar zabiya.

Gwamnatin Nigeria dai ta yi alkawarin biyan asibitin na Abuja kudin duk irin maganin da masu larurar zabiyar za su karba.