An hana gyaran gira a Iran

Iran ta hana maza kwalliyar gira, da gyaran jiki, da zanen jiki wato tattoo.
Bayanan hoto, Iran ta hana maza kwalliyar gira, da gyaran jiki, da zanen jiki wato tattoo.
An wallafa

A kasar Iran, an yi wa wanzamai gargadi a kan yi wa maza gyaran gira.

Kungiyar wanzaman kasar ta yi wa 'ya'yanta gargadin cewa gyaran gira ya saba ka'idar addinin Musulinci, wacce ita ce doka a kasar.

Dokar kuma ta yi hani da zanen kwalliyar jiki, wato Tatto.

Jami'an Iran sun yi kokarin kaddamar da dokar hana kwalliyar maza--irin su halawa da gyaran gashi na yayi mai kuma yanayi da kwalliyar nasara--amma ta kasa hana samarin kasar inda a kullum masu bin yayin nasarar karuwa suke yi.