An rusa hukumar magunguna a Ghana

Asalin hoton, Reuters
An wallafa
Shugaban kasar Ghana John Mahama ya rusa hukumar dake sa ido a kan harkar magunguna a kasar.
Wannan mataki ya zo be bayan wasu rahotanni da aka bayar masu karo da juna a kan magungunan da aka kwace a filin jirgin sama na London.
Kamfanin na kasar Ghana ya ce ya hada hannu da hukumomin Brittaniya wajen cafke wata Mata 'yar kasar Ghana wadda aka samu da hodar iblis kilo goma sha-biyu da rabi.
To amma Jakadan kasar Ghana a Brittaniya ya musanta haka, yana mai cewar, hukumomin Brittaniyar ne suka yi aikisu su kadai.
Fadar Shugaban kasar Ghana ta musanta zargin cewar Matar tana da alaka da Iyalin Shugaban kasar kuma tana tafiyar ne da fasfo na jami'an diplomasiyya.






















