Boko Haram:Wasu mata sun tsere daga Gwoza

Rikicin Boko Haram ya raba dubban mutane da muhallansu
Bayanan hoto, Rikicin Boko Haram ya raba dubban mutane da muhallansu
An wallafa

Rahotanni daga garin Gwoza da ke jihar Borno na cewar wasu mata sun kubuta daga garin wanda ke karkashin ikon kungiyar Boko Haram.

A cewar matan suna cikin wani irin mawuyacin yanayi tun lokacin da 'yan Boko Haram suka kwace garin suka kafa tutocinsu.

Daya daga cikin matan ta shaidawa BBC cewar "'Yan Boko Haram suna tara mutane su rufe wasu a daki, wasu kuma a kaisu kurkuku."

Ta kara da cewar "Suna daurawa mata aure da mayakansu sai su bada sadaki, sun daurawa mata 40 zuwa 50 aure."

A cikin watan Agusta ne, shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, ya yi ikirarin cewa, garin Gwoza da suka kwace daga hannun dakarun Nigeria, a yanzu ba ya karkashin gwamnati ya koma karkashin daular musulunci.