Villas-Boas zai koma St. Petersburg

Asalin hoton, Reuters
An wallafa
Tsohon manajan Tottenham da kuma Chelsea, Andre Villas-Boas ya rattaba hannu a yarjejeniya ta shekaru biyu tare da Zenit St Petersburg.
Manajan mai shekaru 36 wanda Spurs ta kora a watan Disamba, zai maye gurbin Luciano Spalletti a kulob din na Rasha.
"Mr. Villas-Boas zai fara aiki da Zenit St Petersburg a matsayin sabon kocinta a ranar 20 ga watan Maris da muke ciki." A cewar wata sanarwa a shafin intanet na kulob din.
Tottenham ta kori Villas-Boas ne bayan kulob din ya kasa cin nasara a gasar champions league.






















