An gano mota dauke da sinadarin nukiliya

An wallafa
Hukumomi a kasar Mexico sun gano wata babbar motar dibar kaya dauke da sinadarin makamashin nukiliya da aka sace a ranar Talata a wajen birnin kasar.
Hukumomi Sun bayyana cewa Sinadarin Makamashin da aka gano da ake kira Cobalt-60 an fito dashi daga cikin gidansa na kariya.
Hukumomin sun ce barayin da sukai satar na fuskantar barazana ga rayukansu, sai dai hakan ba zai haifar da barazana ga lafiyar jama'ar da ke zaune a wurin ba.
Babbar motar dai na dauke da sinadarin gashin kashi ne da ta dauko daga wani asibiti da ke birnin Tujuana.
Ddireban motar ya ce wasu mutane guda biyu ne suka kwace motar a lokacin da yake shan mai, kuma ta yiwu sun san abinda ke cikin motar.





















