Ana bore kan leken asiri a Amurka

An wallafa
Wasu masu fafutuka dake neman gwamnati ta kawo karshen leken asirin da hukumar tsaron kasa ke yi wa jama'a sun yi wani taron gangami na bore a birnin Washington na Amurka.
Wadanda suka shirya taron gangamin da suka kira "A daina sa ido kan mu" sun ce kawo yanzu sun samu sa-hannun mutane fiye da rabin miliyan a takardar kokensu.
Har ila yau kuma sun bukaci majalisar dokokin Amurkar ta binciki iyakar da shirin leken asirin na hukumar tsaron kasar ya kai a fallasar da tsohon jami'in leken asiri Edward Snowden ya yi wa kasar.
Batun leken asirin nan dai ya haddasa rashin jituwa tsakanin Amurkar da dadaddun aminnan ta a kasashen Turai.






















