'Yan sanda sun saki tsohon gwamnan Zamfara

An wallafa
Rundunar 'yan san dake jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta sallami tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima bayan tayi masa tambayoyi dangane da wani shirin Rediyon tarayya dake Kadunan.
Tsohon gwamnan ya je Kaduna ne inda ya shiga wani shirin gidan rediyo, kuma 'yan sanda suka ce, yayi wasu kalamai da suka yi kama da zuga jama'a.
Kimanin sa'a biyu Sanata Sani Yerima ya kwashe a Hedikwatar ta 'yan sanda.
Sanata Ahmed Sani Yerima dai jigo ne a kokarin kafa jam'iyyar adawa ta APC.






















