Ana zabe a kasar Kenya

Tun da karfe shida ne agogon Kenya, mutane da dama suka fito domin kada kuri'a
Bayanan hoto, Tun da karfe shida ne agogon Kenya, mutane da dama suka fito domin kada kuri'a
An wallafa

Al'ummar kasar Kenya na babban zabe, abin da masana ke kallo a matsayin zabe mafi mahimmanci a tarihin kasar.

Wannan ne karo na farko da ake zabe a kasar, tun bayan da aka yi garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar domin kaucewa irin tashin hankalin da ya auku a kasar bayan zaben da aka gudanar a shekarar ta 2007.

Sama da mutane 1,000 ne da ba basa ga maciji da juna suka rasa rayukansu, bayan rikicin da ya barke a wancan lokacin.

Duk da cewa dai an yi ganganmi neman zaman lafiya, rahotanni sun ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a kusa da Mombasa da safiyar ranar Litinin.

Jami'ai sun ce wasu gungun mutane ne suka kaiwa 'yan sandan hari, a yankin Changamwe a bayan garin Mombasa.

Al'ummar Kenya za su zabi, 'yan majalisa da gwamnonin lardi da kuma yan majalisun lardi.

Sai dai duniya ta sanyan ido ne a kan zaben shugaban kasa.

'Yan takara takwas ne ke neman kujerar shugaban kasa, amma yan takarar dake gaba-gaba sune fira minista mai ci a yanzu, Raila Odinga da kuma Uhuru Kenyatta.