Palasdinawa na tururuwar shiga Masar

Asalin hoton, AP
An wallafa
Kasar Masar ta dan sassauta ka'idojin kai-kawo a iyakar Rafah da ta hada ta da yankin zirin Gaza. Wannan ya ba Falasdinawa masu yawa damar tsallaka iyakar.
Masar da Isra'ila dai sun kulle iyakar ne, tun bayan da kungiyar Hamas ta Falasdinawa, ta karbe iko da Gaza shekaru hudu da suka wuce.
Sai dai har yanzu ba za a gudanar da harkokin kasuwanci a iyakar ta Rafah ba.
Wani wakilin BBC a yankin ya ce, wata alama ce ta sauyin manufa a Masar, bayan an hambarar da shugaba Hosni Mubarak.
Amma Isra'ila har yanzu tana kan bakanta na cewa, kulle iyakar na da mahimmancin gaske, domin zai yi rigakafin sumogal din makamai.





















