Osama ne ke jagorantar Al-Qaeda har lokacin rasuwarsa

An wallafa

A karon farko Manyan jami'an hukumar leken asirin Amurka sun ce Osama Bn Laden ne ke gudanar da aiyukan kungiyar Al- Qaida har zuwa lokacin rasuwar sa.

Wadannan kalamai dai sun saba da wanda hukumar ta bayyana a baya, inda ta ce ana farautarsa ne kurum, ba shine ke gudanar da aiyukan kungiyar ba.

Jami'ai sunce gidan da aka kashe Osama bn Laden a Pakistan, nan ne ake gudanar da aiyukan kungiyar Al- Qaidan, kuma a nan cibiyar ta take.

Hukumomin Amurkan sun kuma saki wasu hotunan bidiyo guda biyar da aka debo daga gidan da jagoran Kungiyar Al- Qaidan ya zauna.

Sun ce farmakin da aka kai ne ya basu damar tattara abubuwa na sirri da ba'a taba samun irinsu ba, daga wani mutum kwaya daya tal da ake zargin shi dan ta'adda ne.

Daya daga cikin hotunan bidiyon da aka debo din ya nuna Osama Bn Laden yana jawabi ga mutanen Amurka.

Sai dai ba'a iya jin abinda yake fada a hoton bidiyon

Daya kuma ya nuna Osama Bin Laden zaune, da bargo rataye a kafadarsa, yana kallon wani shiri a talabijin.

Ba'a dai san takamaimai abinda yake fada a cikin hotunan bidiyon ba, saboda Amurkan ta cire sautin dake cikinsu.

Akwai yiwuwar kungiyar Al- Qaida zata saki wadannann faya- fayan bidiyo ga jama'a nan bada jimawa ba, tare da sautin dake cikinsu.