Hukumomin Nijar na tuntubar makwabta kan satar Faransawa

An wallafa

Gwamnatin Nijar tace, tana tuntubar wasu kasashe makwabta, a kokarin da ake na gano wasu mutane bakwai da aka sace, a yankin arewacin kasar.

A daren Laraba zuwa Alhamis ne, wasu mutane a cikin motoci, dauke da makamai, suka sace mutanen bakwai.

Mutanen sun hada da Faransawa biyar, da kuma bakaken fata 'yan Afirka su biyu, a yankin Agadez.

Wadanda aka sacen ma'aikata ne a kamfanin makamashin nukiliya na AREVA na Faransa, mai aikin hakar ma'adanin uranium a Arlit.