Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Jota zai yi jinya bayan rauni a wasan Liverpool da Inter Milan
Mai horar da Liverpool Jurgen Klopp ya tabbatar da cewa Diogo Jota ya samu rauni a wasansu da Inter Milan a San siro.
An canza Jota ne jim kadan bayan dawowa hutun rabin lokaci, bayan da aka lura ya samu rauni a gwuiwarsa.
Roberto Firmino da ya canje shi ya ci kwallon farko a wasan, kafin Mohamed Salah ya ci ta biyu.
A cewar Klopp '' na ji dadin komai a wasan in banda raunin da Diogo ya samu.''
Jota na taka rawa sosai a kokarin Liverpool na gwada sa'ar cin kofin gasar Premier League, da kofin zakarun turai, da kofin kalubale na FA da kuma na Carabao.
Dan kasar Focugal din ya ci kwallaye 17 a kakar wasannin da ake ciki, kuma Klopp na fatan zai murmure da wuri don Liverpool na da wasan karshe na kofin Carabao da Chelsea a Wembley ranar 27 ga watan Fabrairu.
Sai dai Liverpool ta yi sa'a don a watan Janairu ta saye dan wasan gaban Colombia da FC Porto Luiz Diaz, wanda shima ya haska a wasan na ranar Laraba da Inter Milan.
Liverpool za ta kara da Norwich ne a gasar Premier League ranar Asabar a Anfield, kuma za ta karbi bakuncin Inter Milan a zagaye na biyu na gasar zakarun turai ranar 8 ga watan Maris.