Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Salah da Firmino sun kwatar wa Liverpool maki uku hannun Inter Milan
Liverpool ta kwaci maki uku a gidan Inter Milan, a zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun turai.
Wasan ya tashi 2-0, kuma bakin sun ci kwallayen ne ta hannun Roberto Firmino da Mohamed Salah.
Firmino wanda ya canji Diogo Jota ne ya fara cin kwallo a minti na 75, kadin Salah ya saka ta biyu minti bakwai a tashi wasan.
La'akari da cewa babu dokar ninka kwallon da baki suka ci a waje wato away goal, Liverpool na bukatar tsare gida da kyau da kuma kokarin cin wasu kwallayen a ziyarar da Inter Milan za ta kai musu wata mai zuwa.
Sakamakon na nufin Inter Milan na da jan aiki a gabanta, don tana bukatar cin kwallo uku ba tare da an saka mata ko daya ba a Anfield.
A daya wasan Bayern Munich ta tashi kunnen doki 1-1 da Red Bull Salzburg a Austria.
Masu masaukin bakin sun taka rawar gani sosai ganin cewa shine karon farko da suka taba zuwa wannan mataki, don sai a minti na karshe aka farke kwallon da suka ci.
Red Bull ta ci kwallonta ne ta hannun Junior Adamu a minti 21 da fara wasa, to amma Bayern Munich ta farke a minti na 90 ta hannun Kingsley Coman.
A zagaye na biyu na wasan Red Bull Salzburg za ta kai ziyara filin Allianz arena da ke birnin Munich.