Faransa ta gayyaci Konate na Liverpool a karon farko

Asalin hoton, BBC Sport
Didier Deschamps ya bai wa mai tsaron bayan Liverpool Ibrahima Konate goron gayyata a karon farko zuwa tawagar Faransa, don maye gurbin Raphael Varane.
Varane dan wasan Manchester United ya ji rauni a gasar Nations League da Denmark ta yi nasara da ci 2-1 ranar Juma'a.
Kylian Mbappe sai canji shi aka yi a karawar, sakamakon ciwon gwiwa a fafatawar da suka yi a Stade de France, mataimakin koci, Guy Stephan ya ce za a auna girman raunin dan wasan Paris St Germain.
Konate ya je Liverpool da kafar dama, bayan da ya koma buga gasar Premier League daga RB Leipzig a bara.
Mai shekara 23, ya yi wasa 29 a kungiyar Anfield a dukkan fafatawa karkashin Jurgen Klopp a kakar 2021/22 da cin kwallo uku da wasa 10 kwallo bai shiga ragar Liverpool ba.
Haka kuma Konate ya buga wasan karshe a Champions League da Real Madrid ta ci 1-0 ranar Asabar a Faransa, karon farko da dan kwallon ya buga wasan da Liverpool ta yi rashin nasara.
Faransa za ta ziyarci Croatia ranar Litinin da kuma fafatawa da Austria, kafin ta kara karawa da Croatia a gasar ta Nations League.





















