Manchester City 4:3 Real Madrid: A wasa na biyu za a tantance gwana

An wallafa

Manchester City ta yi nasara a kan Real Madrid da ci 4-3 a Champions League zangon farko a daf da karshe da suka kara ranar Talata a Etihad.

Wadanda suka ci wa Manchester City kwallayen sun hada da Kevin de Bruyne da Gabriel Jesus da Phil Foden da kuma Bernardo Silva.

Ita kuwa Real Madrid ta ci kwallayen ta hannun Vinicius Junior, sannan Karim Benzema ya zura biyu a raga har da daya a bugun fenariti.

Wannan shine wasa na bakwai da suka kara a Champions League, inda City ta ci uku, Real ta yi nasara a biyu da canjaras biyu.

Manchester City za ta ziyarci Real Madrid ranar 4 ga watan Mayu, domin buga wasa na biyu a Santiago Bernabeu.

A rranar za a tantance wadda za ta kai wasan karshe, domin fuskantar Liverpool ko kuma Villareal.

Liverpool ta karbi bakuncin Villareal, domin buga wasan farko a daf da karshe a gasar ta Zakarun Turai ranar Laraba a Anfield.

Real Madrid ce kan gaba a yawan lashe Champions League 13 jumulla, ita kuwa City ba ta taba dauka ba.

Wannan shi ne karo na uku da City ta buga daf da karshe a gasa hudu baya, yayin da Real ta yi wasa na 10 a daf da karshe a fafatawa 12 baya a Champions League.

Rabon da Real Madrid ta lashe Champions League tun kakar 2018, bayan da ta doke Liverpool a wasan karshe da ci 3-1.

'Yan wasan Real Madrid da suka fuskanci City:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Fuidias.

Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo da F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco da Camavinga.

Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Bale, Vini Jr. da Rodrygo.

Wasannin da aka buga tsakanin City da Real:

Champions League Talata 26 ga watan Afirilun 2022

  • Man City 4 - 3 Real Madrid

Champions League Juma'a 7 ga watan Agustan 2020

  • Man City 2 - 1 Real Madrid

Champions League Laraba 26 ga wwatan Fabrairun 2020

  • Real Madrid 1 - 2 Man City

Champions League Laraba4 ga watan Mayun 2016

  • Real Madrid 1 - 0 Man City

Champions League Talata 26 ga watan Afirilun 2016

  • Man City 0 - 0 Real Madrid

Champions League Laraba 21 ga watan Nuwambar 2012

  • Man City 1 - 1 Real Madrid

Champions League Talata 18 ga watan Satumbar 2012

  • Real Madrid 3 - 2 Man City