'Yan wasa shida za su bar sansanin tawagar Italiya

Jorginho
An wallafa

Kimanin 'yan wasa shida ne za su bar sansanin tawagar Italiya, bayan da kasar ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya.

Marco Verratti da Jorginho suna daga cikin shidan da za su bar sansanin, bayan da Italty ba za ta buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022 ba.

Tuni dai Ciro Immobile da Lorenzo Insigne da Domenico Berardi da Gianluca Mancini suka koma kungiyoyinsu donin ci gaba da taka leda in ji DFA.

Koda yake Berardi da Gianluca Mancini na dauke da rauni, za su yi jinya.

Ana sa ran koci Roberto Mancini zai gayyato wasu 'yan kwallon, domin buga wasan sada zumunta da Turkiya ranar Talata.

Ranar Alhamis Arewacin Macedonia ta doke Italiya 1-0 a Palermo a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya a bana.

Italiya mai rike da kofin Euro 2020, wadda karon farko ta sha kashi a gida a wasan cike gurbin shiga gasar kofin duniya a tarihi, ba ta je wadda aka yi a Rasha a 2018 ba.

Ranar Litinin Italia za ta je Konya domin buga wasan sada zumunta da Turkiya ranar Talata.