Afcon 2021Comoros za ta kara da Kamaru ba tare da Gola ba

Comoros Keepers
An wallafa

Ranar Litinin Comoros za ta buga wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka da za ta fafata da Kamaru ba tare da wani daga cikin masu tsaron ragarta ba.

Babban golan tawagar, Salim Ben Boina ya ji rauni a wasan karshe a rukuni na uku, yayin da sauran biyun masu jiran ko-ta-kwana Ali Ahamada da Moyadh Ousseini sun kamu da cutar korona.

Dokar gasar cin kofin Afirka ta fayyace cewar idan 'yan wasa 11 na tsaye ba tare da rauni ko kamuwa da cutar ba, ya zama wajibi su buga karawar da ke gabansu.

Mai horar da masu tsaron ragar Comoros, Jean-Daniel Padovani ya sanar cewar za su zabi wani daga cikin 'yan wasa ya kama gola.

Comoros wadda take ta 132 a jerin kasashen da ke kan gaba a tamaula a duniya na fama da fuskantar kalubalen cutar korona, bayan da ta kama wasu 'jami'ai da 'yan wasa 12.

Fitattun 'yan wasan da ba za su buga mata karawa da Kamaru ba, sun hada da mai tsaron baya, Kassim Abdallah da Alexis Souahy da mai buga tsakiya, Nakibou Aboubakari da Yacine Bourhane da kuma mai cin kwallo Mohamed M'Changama.

Shi kansa kociya, Amir Abdou ya killace kansa, bayan da ya kaamu da annobar.

Wannan shine karon farko da Comoros ke buga gasar kofin Afirka, sannan ta kai zagaye na biyu, wadda ta yi ta uku a rukuni na uku, bayan da ta ci Ghana 3-2.