Afcon 2021: Cameroon ta ja ragamar rukunin farko, bayan 1-1 da Cape Verde

An wallafa

Mai masaukin baki, Kamaru ta ja ragamar teburin rukunin farko a gasar cin kofin Afirka, bayan da ta tashi 1-1 da Cape Verde ranar Litinin.

The Indomitable Lions ce ta fara cin kwallo ta hannun kyaftin Vincent Aboubakar a minti na 39, kuma na biyar da ya zura a raga a gasar bana.

Cape Verde ta farke a minti na takwas da komawa zagaye na biyu ta hannun Garry Rodrigues, wanda ya shiga karawar daga baya.

Kamaru wadda rabon a doke ta a babban birnin kasar tun 1988 za ta ci gaba da fafatawa a Yaounde a wasannin zagaye na biyu tsakanin wadda ta yi ta uku a rukuni na uku ko na hudu ko kuma na biyar da za ta kara ranar Litinin 24 ga watan Janairu.

Cape Verde ta kare a mataki na uku da maki hudu, bayan da Burkina ce ta biyu, watakila Cape Verde ta buga fafatawar zagaye na biyu mai makin hudun.

A gasar kofin Afirka da aka yi a Masar a 2019, maki hudu ya isa ya kai tawaga buga zagayen gaba, kamar dai yadda aka yi a gasar cin kofin nahiyar Turai a 20016 da 2020.

Kyaftin din Kamaru, Aboubakar mai shekara 29 ya yi kan-kan-kan da Samuel Eto'o wanda ya ci kwallo biyar a Afcon.

Eto'o mai tarihin cin kwallo 18 a raga a wasannin Afcon ya zura biyar a raga a gasa biyu, wato a 2006 da kuma 2008.

Kamaru za ta fara buga zagaye na biyu a gasar da take karbar bakuncinar Litinin, saboda haka da sauran tafiya a gabanta, kila Aboubakar ya haura tarihin cin kwallo sama da biyar kenan.