An kara tuhumar Benjamin Mendy da laifin fyade

An wallafa

An kara tuhumar dan kwallon Manchester City, Benjamin Mendy da laifin fyade.

Kawo yanzu ana tuhumar dan wasan tawagar Faransa da zargin fyade karo bakwai da na cin zarafi.

An tuhumi dan wasan mai shekara 27 a baya-bayan nan kan karin laifin da ya aikata, kuma Mendy ya gurfana a gaban kotun da ke Chester Crown don saurararen kararrakin.

Wannan tuhumar da aka kara yi masa an ce ya aikata laifin a Yulin 2021.

Sauran tuhumarsa da aka yi ya aikata laifukan tsakanin Oktoban 2020 zuwa Agustan 2021.

Tun cikin watan Agusta aka tsare Mendy, wanda ya gurfana tare da Louis Saha Mattuire na Eccles a Greater Manchester.

An tuhumi dan wasan Manchester City tun farko da laifin aikata fyade karo shida da cin zarafi.

An ci gaba da tsare mutanen biyu, bayan da aka saurari karar ta minti 40 a HMP Altcourse a Liverpool.

Bayan da aka tsara zaman kotu cikin watan Janairu, an rage ranakun, bayan da wasu tuhume tuhume ke kara bayyana.

Mendy wanda ya buga Premier League a bara ya koma kungiyar Etihad tun 2017 daga Monaco kan fam miliyan 52.