Shirin Fifa na gudanar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekara bibiyu zai samar da fam biliyan 3.3

France celebrating winning the World Cup in 2018
Bayanan hoto, Faransa ce ta lashe kofin duniya a Rasha a 2018, Qatar ce za ta karbi bakuncin gasa ta gaba a 2022.
An wallafa

Gasar kofin duniya duk bayan shekara bibiyu za ta samar da fam biliyan 3.3, fiye da kudin da ake samu duk bayan shekara hudu in ji hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa.

Fifa na fatan kawo sauyi don saukaka wasannin tamaula da ake yi a shekara- shekara.

An gayyaci dukkan mambobin hukumar su 211 don tattaunawa da Arsene Wenger da aka bai wa wuka da nama wajen bunkasa wasannin gasar cin kofin duniya.

To sai dai kuma kuma hukumar kwallon kafar Turai da ta Kudancin Amurka na adawa da tsarin.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf ta goyi da bayan wannan sabon shirin da ake son cimma.

An sanar da wakilan cewar kudin da za a samu a kallon wasannin da na bai wa kafafen yada labarai damar kwarmata gasar da kamfanoni da ke tallata wasanni, idan za a yi duk bayan shekara bibiyu, za a iya samun kudin shiga daga fam biliyan 5.3 da ake sama a baya zuwa fam biliyan 8.6 da kasashe 48 za su fafata daga 2026.

Cikin binciken da aka gudanar ta hannun Nielsen Sports, wani kamfanin Jamus da ya kware wajen binciken kididdiga da harkar gudanarwa ya ce wasannin ba za su nakasa kudin shiga da ake samu daga lik-lik na kasashe ko manyan wasanni da suka hada da Champions League da suke kukan za su yi hasarar kudin shiga.

A taron an kuma sanar da mambobi cewar a kalla za a bai wa kowacce kasa kudi da zai kai fam miliyan 12.1 karin kudin shiga, sai dai ba a fayyace tsarin da za a bi wajen raga kudaden ba.

Wenger ya daura aniyar rage gibin da ke tsakanin kasashen da ke da arziki da matalauta da samar da tsarin 'yan wasa daga matalautan kasashe za su samu damar nuna kansu a duniya a sana'ar tamaula.

Wani rahoto da taron lik-lik na duniya ya fitar ya ce, tsarin da Fifa ke son gudanarwa zai sa wasannin gida da na Zakarun Turai ya kai Yuro biliyan takwas, kudin gudanarwa a kowacce kaka.

Ranar Juma'a Uefa ta wallafa wani rahoto da wani kamfani Oliver & Ohlbau ya wallafa da cewar nahiyar Turai za ta yi hasara tsakanin Yuro biliyan 2.5 zuwa uku tsakanin mambobinta a shekara hudu.