An yi wa Benjamin Mendy karin tuhama biyu

Benjamin Mendy
Bayanan hoto, Benjamin Mendy ya koma Manchester City da taka leda a 2017 kan yarjejeniyar fam miliyan 52
An wallafa

An kara yi wa mai tsaron bayan Manchester City, Berjamin Mendy karin tuhuma biyu kan fyade.

Wata kotun majistare a Stockport ta bukaci Mendy ya gurfana a gabanta ranar Laraba.

Mai shekara 27, wanda har yanzu ke tsare na fuskantar tuhuma shida kan fyade da cin zarafi.

Tuhamar ta hada da korafin da wata 'yar shekara 16 ta yi kan zargin laifukan da ya aikata tsakanin Oktoban 2020 zuwa Agustan 2021.

Dan kwallon tawagar Faransa ya buga wasannin Premier League a bara da Manchester City ta lashe kofin, kungiyar da ya koma taka leda a 2017 kan fam miliyan 52.

Manchester City ta dakatar da dan wasan tun bayan da 'yan Sanda suka tuhumeshi har sai sun kammala bincike.

Haka kuma ana tuhumar Louis Saha da zargin fyade a laifin da aka ce ya aikata tsakanin Maris din 2021 zuwa Agustan 2021.

An kuma tuhumi Saha mai shekara 40 da karin wasu laifi biyu da suka hada da fyade da cin zarfi, an umarci ya gurfana a kotu,

Ana sa ran mutanen biyu za su gurfana gaban shari'a ranar 24 ga watan Janairun 2022.