Emmanuel Amuneke: Wata rana zan koyar da kwallon kafa a Turai

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan kwallon tawagar Najeriya, Emmanuel Amuneke ya ce har yanzu bai fitar da ran zai koyar da tamaula nan gaba a Turai ba.
Amuneke na ta kokarin ganin ya horar da kwallon kafa a Spaniya, sai dai kawo yanzu sunki ba shi dama.
Mai shekara 49 ya ja ragamar Tanzaniya a karon farko zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka tun 1980 da ta fafata a gasar.
Amuneke na neman kungiyar da zai ja ragama a horar da kwallon kafa, tun bayan da ya bar Misr El-Makkasa ta Masar.
Ya kuma jagoranci tawagar Najeriya ta matasa 'yan kasa da shekara 17 zuwa Chile a 2015.
A lokacin da ya buga wa Najeriya tamaula ya lashe lambar zinare a wasannin Olympic a 1996, ya kuma lashe kofin Afirka da buga gasar kofin duniya, ya kuma zama fitatcen dan kwallon nahiyar.
''Abin takaici bayan da na buga wasanni a Spaniya da karatun koci a kasar, amma ba a bai wa dan Afirka damar koyar da kwallon kafa a Spaniya,'' kamar yadda Amuneke ya sanar da BBC.
A kwanaki an tuntubi Amuneke da Seyi Olafinjana kan aikin daraktan horar da kwallo a hukumar tamaula ta Najeria, amma ba su amince da tayin ba.
A watan jiya ne aka bai wa Austin Eguavoen aikin.

























