Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jordan Ayew: Dan wasan Crystal Palace ya kamu da cutar korona
Dan kwallon Crystal Palace, Jordan Ayew ya kamu da cutar korona kamar yadda koci Roy Hodgson ya tabbatar.
Dan wasan mai shekara 29 ya kamu da cutar ranar Juma'a, ya kuma kasance da tawagar Ghana a tsakanin lokacin da aka ware don buga wasannin kasa da kasa.
Bai kuma buga wasan da Palace ta yi 1-1 da Brighton ba ranar Lahadi a gasar Premier League.
Dokar gwamnati ta bukaci duk wanda ya kamu da annobar ya killace kansa kwana 10 daga nan a sake gwada shi kafin ya koma atisaye.
Shima takwaran Ayew, Bernard Mensah ya kamu da cutar korona, bayan da ya koma kungiyar Besiktas daga kammala wasannin kasa da kasa.