Premier League: Kungiyoyi za su fara atisayen bai daya

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin Premier sun amince za su fara atisaye na 'yan wasa bai daya za kuma su iya hada jiki a shirye-shiryen da ake yi na ci gaba da gasar bana.
Haka kuma sun yadda 'yan kwallo za su ci gaba da atisaye cikin rukuni za kuma su iya hada jiki, amma a kiyaye cudanyar da ba ta zama wajibi ba.
Kungiyoyin za kuma a ci gaba da tattaunawa don zakulo hanyoyin da suka dace a karkare gasar 2019-20.
Haka kuma za a ci gaba da gwajin cutar korona ga 'yan wasa da jami'ai sau biyu a kowanne mako.
Kawo yanzu an samu 'yan wasa takwas dauke da annobar, bayan gwajin mutun 1,744 da aka yi wa masu hulda da gasar Premier, ana kuma sa ran bayyana sakamakon zango na uku na gwajin.
A makon jiya aka amince 'yan wasa su yi atisaye cikin rukuni ba tare da hada jiki ba, kuma a karon farko tun bayan da aka dakatar da Premier League ranar 13 ga watan Maris saboda bullar cutar korona.
Ranar Alhamis kungiyoyin za su ci gaba da tattaunawa kan filayen da za a yi wasanni da yadda ya kamata a karkare kakar bana idan an ci karo da takaddama da sauransu.
Haka kuma dokar nan ta bayar da tazara na nan da sa takunkumin kare fuska da sauran matakan da gwamnati ta dauka don gudun yada annobar

























