Klinsmann ya ajiye aikin horas da Hertha Berlin

Asalin hoton, Getty Images
Jurgen Klinsman ya ajiye aikin horas da Hertha Berlin zai ci gaba da aikin jami'in sa ido a harkokin kungiyar.
Klinsman tsohon dan wasan Bayern Munich da tawagar kwallon Jamus, ya karbi aikin kocin Hertha cikin watan Nuwamba, bayan da aka kori Ante Covic.
Tsohon kocin tawagar kwallon Amurka, mai shekara 55 ya ja ragamar wasa 10 a Hertha, inda ya ci karawa uku da rashin nasara a wasa hudu.
A lokacin da ya karbi aikin kungiyar tana kasan teburi da maki iri daya da na Fortuna Düsseldorf, yanzu ta bar gurbin da tazarar maki shida.
A farkon watan Nuwamba aka nada Klinsman a cikin mahukuntan Hertha, daga baya aka ba shi aikin jan ragamar kungiyar.
Hertha za ta buga wasanta na gaba a Bundesliga ranar Asabar a gidan Paderborn, kuma Alexander Nouri ne zai yi aikin rikon kwarya.





















