Golan Tottenham, Lloris ya gama buga wasa a 2019

Tottenham
An wallafa

Mai tsaron ragar Tottenham, Hugo Lloris zai yi jinya har zuwa 2020, bayan da ya yi rauni a kafada a lokacin da yake buga wa kungiyarsa wasan Premier a karshen mako.

Mai tsaron ragar tawagar Faransa ya yi rauni ne a lokacin da ya yi kokarin tare wani kwallo a fafatawar da Brighton ta ci Tottenham 3-0 a gasar Premier.

A yammacin Asabar Tottenham ta tabbatar da raunin golan, amma ba ta fayyace lokacin da zai kammala jinya ba.

Kyaftin din tawagar Faransa da Tottenham yana cikin 'yan wasan da kasarsa ta gayyata karawar neman shiga gasar kofin nahiyar Turai da za ta yi da Turkiya a makon nan.

Kocin Faransa, Didier Deschamps ya ce za su yi rashin golan mai mahimmaci a tawagar, amma dai yana da Alphonse Areola da Steve Mandanda da kuma Mike Maignan don maye gurbinsa.