Ter Stegen ya buga wa Barcelona wasa 200

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Lahadi Barcelona ta doke Sevilla 4-0 a wasan mako na takwas a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a Camp Nou.
Marc-Andre ter Stegen shi ne ya tsare ragar Barcelonma a ranar kuma wasa na 200 kenan da ya yi wa kungiyar.
Golan dan kasar Jamus, wanda ya koma Camp Nou a 2014 ya lashe kofi 13 a kungiyar.
A kaka biyun nan tun taga 2016, Ter Stegen shi ne ke tsare ragar Barcelona a wasannin Champions League da Copa del Rey, shi kuwa Claudio Bravo ke buga wasannin La Liga.
Ter Stegen ya zama daya daga masu tsaron ragar Barcelona 10 da suka yi mata wasa 200.
Wannan ce kaka ta shida da golan ke tsaron ragar Barcelona, kuma a bana ya taka rawar gani, inda ya tare fenariti a karawa da Borussia Dortnmund a Champions League.





















