Coutinho da Maguire da Dani Alves da Michael Seri a kasuwar sayen 'yan wasa

Philippe Coutinho
An wallafa

Philppe Coutinho ya amince da wata yarjejeniya da za ta ba shi damar komawa Liverpool a matsayin aro na shekara biyu tare da zabin sayansa kan kudi fan miliyan £88, a rahoton Calciomercato.

Manchester United ta amince ta dauki Harry Maguire daga Leicester City kan fan miliyan £80 wanda hakan zai sa ya zama dan wasan baya mafi tsada a duniya.

United za ta fara biyan fan miliyan £60 tukunna, inda daga baya za ta cika milyan £20 kan dan wasan mai shekara 26 dan kasar Ingila, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Harry Maguire

A gefe guda kuma, Telegraph tana cewa dan wasan bai zaku da ya koma Man United ba sannan kuma kungiyarsa ta Leicester tana da kwarin gwiwar zai ci gaba da zama idan dai har ba a biya ta kudin da ya zarta fan miliyan £75 ba a kansa.

Har wa yau, Leicester tana kokarin maye gurbinsa ne da dan wasan Brighton kuma dan kasar Ingila Lewis Dunk, inda ta amince ta biya fan milyan £45 kan dan wasan mai shekara 27, in ji Sun.

Kungiyar Celtic ta yi watsi da tayin da Arsenal ta yi wa dan wasanta mai shekara 22 na baya-bayan nan wato Kieran Tierney, wanda ya kai fan miliyan £25, a cewar rahoton Sky Sports.

Ita kuwa Mirror ta ce Manchester City ta yi imanin cewa Leroy Sane zai ki yarda da komawa Bayern Munich idan suka miko tayin sayan dan wasan mai shekara 23 a hukumance.

Tottenham ta bi sahun Manchester City wurin yunkurin daukar kwararren dan wasa Dani Alves mai shekara 36 bayan ya kasance ba tare da kulob ba lokacin da ya bar PSG a karshen kakar bara. (Mundo Deportivo)

AC Milan ta bi sahun Roma wurin yunkurin daukar dan wasan tsakiyar Fulham da kuma Ivory Coast Jean Michael Seri mai shekara 27, in ji jaridar Express.

Goal ta ruwaito cewa "Atletico ba ta da wata hujja game da ikirarinta cewa Barcelona ta cimma yarjejeniya da Griezmann tun a watan March," in ji shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu.