An ci tarar Paul Scholes saboda karya ka'idojin caca

Paul Scholes
Bayanan hoto, Paul Scholes ya mallaki kaso 10 cikin 100 na kungiayr Salford City a 2014
An wallafa

An ci tarar tsohon dan wasan Manchester United, Paul Scholes fam 8,000, bayan da ya amince ya karya ka'idojin yin cacar kwallon kafa.

An tuhumi Scholes da yin caca kan wasannin tamaula 140 tsakanin 17 ga watan Agustan 2015 zuwa 12 ga watan Janairun 2019.

Haka kuma hukumar kwallon kafar Ingila ta gargadi tsohon dan wasan tawagar Ingila da ya kaucewa sake aikata laifin nan gaba.

Scholes ya ce ''Ina neman afuwa kan laifin dana aikata na kuma amince da tarar da FA ta yi min.

''Wannan kuskure ne dana aikata, ban kuma yi da nufin murda sakamakon wasa ba, kuma na tabbata idan bani da alaka da wata kungiya da na yi caca a kai to babu wata matsala.

Scholes wanda ya yi aikin horas da Oldham Athletic kwana 31 daga baya ya yi ritaya, yana da kaso 10 cikin 100 na mallakar Salford City mai buga gasar League Two a Ingila.