Real za ta ci kofin duniya na hudu

Real Madrid
An wallafa

Kungiyar Real Madrid za ta buga wasan daf da karshe a gasar cin kofin duniya ta Zakarun nahiyoyin duniya da ake yi a Abu Dhabi.

Real Madrid wadda ta lashe kofin Zakarun Turai za ta bugan wasan daf da karshe da Kashima Antlers wadda ta ci kofin nahiyar Asia a ranar Laraba.

Madrid na fatan lashe kofin na duniya na uku a jere na kuma hudu jumulla, bayan da ta lashe a 2014 da 2016 da 2017.

Kuma kungiyoyi bakawi ne ke fafatawa a gasar da ta hada da Zakarun nahiyoyin duniya shida da kuma mai masaukin baki.

World Club Cup